Da Duminsa: Wasu Daga Cikin Daliban Islamiyya da Aka Sace a Jihar Neja Sun Tsere

Da Duminsa: Wasu Daga Cikin Daliban Islamiyya da Aka Sace a Jihar Neja Sun Tsere

  • Wasu daga cikin daliban da aka sace a wata Islamiyya a jihar Neja sun tsere daga hannun 'yan bindiga
  • Malam Abubakar Alhassan, shugaban makarantar ya tabbatar da kubutar daliban mata daga hannun 'yan bindigan

Makarantar Salihu Tanko Islamiyya da ke garin Tegina a jihar Neja ta ce an kara samun karin biyu daga cikin daliban makarantar fiye da 100 da 'yan bindiga suka sace, da suka tsere daga hannu masu garkuwa da su.

Fiye da wata daya ke nan da 'yan bindiga ke garkuwa da daliban galibinsu kananan yara bayan sace su daga makarantar.

Malam Abubakar Alhassan shugaban makarantar wanda ya tabbatar wa BBC da kubutowar daliban ya ce mata ne da suka tsere daga cikin barayin lokacin da suka sace su.

KARANTA WANNAN: APC Ta Yi Zazzafan Martani Kan Shirin Maguɗin Zaɓen 2023, Ta Bankaɗo Wani Sirrin PDP

Da Duminsa: Wasu Daga Cikin Daliban Islamiyya da Aka Sace a Jihar Neja Sun Tsere
Allo a cikin ajin makarantar Islamiyya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Ya ce tun lokacin, sai yanzu Allah ya dawo da yaran gida. Kuma yarinya daya ce ta fara dawo wa kafin kuma aka sake samun ta biyu.

A cewarsa:

“Ɗaya yarinyar tana asibiti, kuma kamar ta samu taɓin ƙwaƙwalwa domin ta kasa gane gidansu."

Mutum 15 cikin waɗanda aka sace a harin Islamiyyar Tegina sun gudo bayan masu tsaronsu sunyi tatil da giya

Wasu mutum 15 cikin wadanda yan bindiga suka sace a yayin da suka kai hari makarantar Islamiyya a Tegina, jihar Niger sun tsere daga hannun masu garkuwa a lokacin da masu tsaronsu suka yi tatil da giya, Daily Trust ta ruwaito.

Wadanda suka gudo din manya ne da aka sace tare da dalibai 156 a makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko a cikin watan Mayu.

The Nation ta ruwaito cewa wasu majiyoyi a garin sun ce an raba mutanen da daliban sannan aka kai su wani daji da ke jihar Zamfara bayan sace su.

KARANTA WANNAN: Bayan Zarge-Zargen PDP Cewa APC Na Shirya Manakisa, APC Ta Mayar da Martan

An Sako 11 Cikin Ɗaliban Islamiyya Da Aka Sace a Neja

A wani labarin, An sako dalibai 11 cikin wadanda yan bindiga suka sace a wani makarantar Islamiyya da ke Tegina a karamar hukumar Rafi na jihar Niger, Channels Television ta ruwaito.

Babban sakatariyar watsa labarai na gwamnan jihar Niger, Mary Noel-Berje ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar.

A cikin sanarwar da ta fitar a daren ranar Lahadi, Ms Noel-Berje ta ce yan bindigan sun lura cewa yaran sunyi kankanta ne kuma ba za su iya tafiya ba hakan yasa suka sako su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel