Da Ɗuminsa: An Sako 11 Cikin Ɗaliban Islamiyya Da Aka Sace a Neja

Da Ɗuminsa: An Sako 11 Cikin Ɗaliban Islamiyya Da Aka Sace a Neja

- Yan bindigan da suka sace daliban makarantar Islamiyya a Tegina jihar Neja sun sako 11 daga cikinsu

- Ms Noel-Berje, sakatariyar watsa labarai na gwamnan jihar Niger ta tabbatar da sakin daliban a daren ranar Lahadi

- Noel-Berje ta ce Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar ya nuna bakin cikinsa kan sace daliban yana mai neman dauki daga gwamnatin tarayya

An sako dalibai 11 cikin wadanda yan bindiga suka sace a wani makarantar Islamiyya da ke Tegina a karamar hukumar Rafi na jihar Niger, Channels Television ta ruwaito.

Babban sakatariyar watsa labarai na gwamnan jihar Niger, Mary Noel-Berje ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar.

Da Duminsa: An Sako 11 cikin Daliban Islamiyya Da Aka Sace a Neja
Da Duminsa: An Sako 11 cikin Daliban Islamiyya Da Aka Sace a Neja. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

A cikin sanarwar da ta fitar a daren ranar Lahadi, Ms Noel-Berje ta ce yan bindigan sun lura cewa yaran sunyi kankanta ne kuma ba za su iya tafiya ba hakan yasa suka sako su.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan

Noel-Berje ta ce Gwamna Abubakar Sani Bello ya bayyana bakin cikinsa game da rahoton sace mutanen da ba-su-ji-ba ba-su-gani-ba da yan bindiga ke yi a kananan hukumomin Rafi, Wushishi da Bida.

Yan bindiga sun kutsa garin Tegina a karamar hukumar Rafi, sun harbe mutum daya har lahira, sun jikkata guda sannan suka sace daliban makarantar Islamiyya da Malamai a Makarantar Salihu Tanko Islamic School da wasu fasinjoji a mota kirar Sharon da ke hanyar zuwa Minna da a yanzu ba a tantance adadinsu ba.

KU KARANTA: An Kama Budurwa Da Saurayi Da Ke Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ta Intanet a Abuja

Da ya ke cigaba da magana kan mummunan lamarin, Gwamna Bello ya ce abin damuwa ganin yadda yan bindigan ke kara bunkasa. Ya jadada rokonsa na neman dauki cikin gaggawa daga gwamnatin tarayya.

Gwamna Bello ya yi kira ga mutanen jihar su kwantar da hankulansu a yayin da gwamnati ke kokarin cigaba da kare rayyuka da dukiyoyin mutanen jihar.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel