NANS Ta Gana da Sheikh Gumi, Ta Buƙaci a Saƙo Ɗaliban da Aka Sace

NANS Ta Gana da Sheikh Gumi, Ta Buƙaci a Saƙo Ɗaliban da Aka Sace

  • Ƙungiyar NANS ta ƙasa ta gana da shahararren malamin nan dake Kaduna, Sheikh Dr. Ahmad Gumi
  • Shugaban ƙungiyar, Sunday Asefon, yace sun tattauna da malamin ne domin ganin an kuɓutar da dalibai
  • Yace ƙungiyar NANS ba zata huta ba har sai ta tabbatar da zaman lafiya ya dawo kamar da a makarantu

Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) ta gana da shahararren malamin addinin islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi, domin tattaunawa kan yadda za'a kuɓutar da ɗaruruwan ɗalibai dake hannun yan bindiga a faɗin ƙasar nan, kamar yadda leadership ta ruwaito.

KARANTA ANAN: APC Ta Shirya Babban Gangami Yayin da Jiga-Jiganta Zasu Dira Jihar Zamfara

Shugaban NANS, Sunday Asefon, shine ya bayyana haka ga manema labarai a wani jawabi da ya fitar ranar Litinin.

Yace sun gana da malamin ne domin ganin an tabbatar da tsaron ɗalibai a dukkan makarantu da kuma yadda za'a kuɓutar da waɗanda ɓarayi suka yi garkuwa da su, kamar yadda punch ta ruwaito.

NANS Ta Gana da Sheikh Ahmad Gumi
NANS Ta Gana da Sheikh Gumi, Ta Buƙaci a Saƙo Ɗaliban da Aka Sace Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

NANS ba zata runtsa ba har sai ɗalibai sun samu tsaro

A jawabin da shugaban NANS ya fitar, wanda aka yiwa take da 'Lafiya da tsaron makarantu: NANS ta gana da Sheikh Gumi,' Asefon yace ƙungiyar ɗalibai ba zata huta ba har sai makarantu sun zauna lafiya.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Hankalin Mutane Ya Tashi Yayin da Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba da Ɗiyar Wani Ɗan Fulani

Yace: "Zamu ƙara ƙaimi mu cigata da tattaunawar sulhu da yan bindiga domin kuɓutar da ɗaliban dake hannun su."

"Zamu yi iyakacin ƙoƙarin mu wajen tabbatar da makarantu sun zauna lafiya, yayin da ɗalibai zasu daina jin tsoro da fargabar kawo musu hari."

"Ba zamu huta ba har sai mun tabbatar zaman lafiya a makarantu, zamu cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin a nemi mafitar da zata dawo da zaman lafiya a makarantu."

A wani labarin kuma COAS Ya Sake Kai Ziyara Borno, Ya Umarci Sojoji Su Ragargaji Yan Boko Haram da ISWAP

Hafsan sojin ƙasa, COAS Farouƙ Yahaya, ya umarci rundunar sojin dake yaƙi a arewa maso gabas da su kawo ƙarshen ta'addanci.

Mr. Yahaya yayi wannan roƙon ne yayin da yakai wata ziyarar aiki ga rundunar operation haɗin kai a Monguno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262