Da duminsa: Kotu ta tsare shahararren jigon APC a gidan kurkuku

Da duminsa: Kotu ta tsare shahararren jigon APC a gidan kurkuku

  • Kotu ta yi umurnin tsare Asekun Kehinde, tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Lagos Island, a gidan kurkuku
  • Mai shari'a Ayokunle Faji na babbar kotun tarayya da ke Legas ne ya ba da umarnin a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, bayan ya saurari wanda ake kara da mai gabatar da kara
  • Kehinde, wanda hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ke tuhuma, an kama shi da laifin mallakar miyagun kwayoyi

An tsare wani jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Lagos Island, Asekun Sakiru Kehinde, a gidan yari saboda fataucin miyagun kwayoyi.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Legas ta bada umarnin a sake garkame Kehinde a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, bayan gurfanar da shi kan zargin fitar da hodar Iblis mai nauyin kilogram 1.000.

KU KARANTA KUMA: Da Dumi-Dumi: Majalisa Ta Amince da N74.78bn a Kasafin Kudin 'Yan Sanda

Da duminsa: Kotu ta tsare shahararren jigon APC a gidan kurkuku
NDLEA na tuhumar Asekun Kehinde, tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Lagos Island daa fataucin miyagun kwayoyi Hoto: NDLEA
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Mai shari'a Ayokunle Faji ya bayar da umarnin ne bayan Kehinde ya ki “amsa laifinsa" kan tuhumar da ake masa guda daya da ta shafi lamarin.

A cewar rahoton, hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ce ta gurfanar da wanda ake karar a kan tuhuma mai lamba FHC/L/99c/2021.

Abu Ibrahim, mai gabatar da kara na hukumar ta NDLEA, ya fadawa alkalin kotun cewa Kehinde ya aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Mayu, a lokacin da ake tantance fasinjoji a jirgin Virgin Atlantic da ya tashi daga Lagos zuwa London, a dakin tashi na Filin jirgin saman Murtala Muhammed, Ikeja Lagos.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai wa ayarin Ganduje hari a hanyar Zamfara

Kotu ta ce jigon jam’iyyar APC Kehinde ya mallaki haramtacciyar kwaya

Kotun ta saurari cewa wanda ake kara, "ba tare da halattaccen izini ba ya fitar da hodar iblis mai nauyin kilogram 1.000, wani magani na kwaya" wanda aka haramta a kasar.

Lauyan wanda ake kara, Olasupo Shasore SAN da ke jagorantar Cif Benson Ndakara, ya sanar da kotu cewa an gabatar da bukatar neman beli a gaban kotun, ya kara da cewa NDLEA ta gabatar da amsa kan bukatar da ake magana a kai.

Shasore ya roki kotu da ta bayar da belin wanda ake tuhumar bisa sharadin sassauci saboda laifin da aka tuhume shi a kai na beli ne.

Sai dai lauyan masu kara, ya ki amincewa da shi, inda ya roki kotu da ta ki amincewa da bukatar belin saboda girman laifin.

Alkalin da ke jagorantar shari’ar ya dage shari’ar har zuwa ranar 16 ga watan Yuli sannan ya bayar da umarnin tsare wanda ake kara a gidan yari.

NDLEA ta yi nasarar cafke dillalan miyagun ƙwayoyi 231 a jihar Oyo

A wani labarin, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, reshen jihar Oyo, ta ce ta kama mutane 231 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi daga watan Yunin 2020 zuwa Yunin 2021, Pulse NG ta ruwaito.

Da ya ke yi wa yan jarida jawabin, a ranar Alhamis game da ayyukan da hukumar ta yi cikin lokacin da ake nazari, Josephin Obi, kwamandan jihar ya ce mutum 215 cikin wadanda ake zargin maza ne yayin da 16 kuma mata.

Mrs Obi, wacce ta samu wakilcin mataimakin kwamanda Anthony Gotar ta kuma ce rundunar ta yi nasarar kwace ganyen wiwi mai nauyin 6,355.74 da wasu kayan maye a cikin watanni shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng