Da Dumi-Dumi: Majalisa Ta Amince da N74.78bn a Kasafin Kudin 'Yan Sanda

Da Dumi-Dumi: Majalisa Ta Amince da N74.78bn a Kasafin Kudin 'Yan Sanda

  • Majalisar dattijai a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, ta amince da naira biliyan 74.78 na Asusun Lamunin 'Yan Sandan Najeriya
  • Wannan ya biyo bayan gabatar da rahotanni daga kwamitocin majalisar dattijai da ta wakilai kan lamuran ‘yan sanda
  • Kudin zai dauke nauyin kudaden da za a kashe wajen kula da harkoki, ciki harda kudaden ma'aikatan rundunar

Majalisar dattawa ta amince da N74,773,601,916.30 a matsayin kasafin kudin 2021 na asusun lamunin rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

Amincewar na zuwa ne bayan gabatar da rahoton kwamitocin majalisar dattijai da na wakilai kan harkokin ‘yan sanda a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai wa ayarin Ganduje hari a hanyar Zamfara

Da Dumi-Dumi: Majalisa Ta Amince da N74.78bn a Kasafin Kudin 'Yan Sanda
Majalisa ta amince da N74.78bn a matsayin kasafin kudi na asusun lamunin 'yan sanda Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Sanata Haliru Dauda Jika, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan sanda, shine ya gabatar da rahoton a ranar Laraba.

A cewar rahoton, an ware N988,279,006.05 daga ciki don kudin ma'aikata, yayin da aka ware N10,027,610,310.25 don gudanar da harkoki sannan aka ware N63,757,712,600.00 don gyare-gyare.

Buhari: Na Bada Umurnin Ɗaukan Sabbin Ƴan Sanda 10,000 da Yi Musu Ƙarin Albashi

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa yan Nigeria tabbacin cewa gwamnatinsa a halin yanzu tana aikin daukan sabbin jamian yan sanda 10,000 domin inganta tsaron kasa, The Channels ta ruwaito.

News Digest ta ruwaito cewa Buhari ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis a jihar Legas yayin ziyarar aiki na kwana daya da ya kai jihar domin kaddamar da wasu ayyuka.

"A halin yanzu muna kan daukan sabbin jami'an yan sanda 10,000 domin karfafa tsaro a sassan kasar," in ji Buhari.
Ya kara da cewa, "Na umurci hukumar kula da albashi na kasa ta kara wa yan sanda albashi da alawus-alawus."

Asali: Legit.ng

Online view pixel