Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai wa ayarin Ganduje hari a hanyar Zamfara

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai wa ayarin Ganduje hari a hanyar Zamfara

  • 'Yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano
  • Maharan sun far masu ne a hanyarsu ta komawa Kano daga Zamfara bayan taron APC da aka yi a ranar Talata, 29 ga watan Yuni
  • Sai dai an ce gwamnan baya cikin ayarin a lokacin da aka far masu

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin‘ yan fashi ne sun kai wa ayarin motocin Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano hari a daren Talata, 29 ga watan Yuni.

Akalla ‘yan sanda uku ne suka samu raunuka a harin wanda ya faru bayan ayarin motocin na kan hanyarsu ta zuwa Kano daga jihar Zamfara, inda aka gudanar da babban taron jam’iyyar APC a ranar Talata, jaridar Aminiya ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Kallon kitse ake yi wa rogo: Bidiyon cikin wata ƴar bukka da ke dauke da katon gado da kayan alatu

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai wa ayarin Ganduje hari a hanyar Zamfara
An tattaro cewa gwamnan baya cikin ayarin a lokacin da aka far masu Hoto: RFI
Asali: UGC

Ganduje na cikin gwamnonin da suka ziyarci Gusau, babban birnin Zamfara, don tarbar Gwamna Bello Matawalle da manyan ‘yan siyasar Zamfara da suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki.

Majiyoyin gidan Gwamnatin sun tabbatar da harin amma sun ce Ganduje baya cikin ayarin motocin lokacin da suka ci karo da ‘yan bindigar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ganduje ya bi ayarin takwaransa na jihar Jigawa, Abubakar Badaru, bayan taron gangamin a Gusau.

Wani jami'in gidan gwamnati wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Kun san saboda wurin ya kasance a cunkushe bayan taron wanda gwamnonin jihohi da dama suka halarta, Mai Girma Gwamna Ganduje tare da abokinsa, Gwamna Badaru sun isa Kano ne sa'o'i kadan kafin ayarin na Kano su iso."

An ce ‘yan bindiga da yawansu wadanda suka tare hanyar, sun bude wuta nan take da suka hango jerin gwanon motocin.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: PDP ta sake rashi na wasu sanatoci 3, sun koma APC

Kokarin jin ta bakin Babban Sakataren yada labaran Gwamnan, Abba Anwar, ya ci tura yayin da wayoyinsa suke a kashe har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

'Karin bayani: Bayan harbe ɗan majalisar Zamfara, an yi garkuwa da ɗansa da direbansa

A wani labari, yan bindiga sun harbe dan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar Shinkafi, Mohammed Ahmed har lahira kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun ce yan bindigan sun kashe Ahmed ne a kan hanyar Sheme zuwa Funtua, wani gari da ke kan iyakar jihar Zamfara da Katsina.

Zamfara da Katsina, jihohin da ke makwabtaka da juna a Arewa maso Yamma na cikin wuraren da yan bindiga suka addaba da hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng