Wata Kungiyar Igbo Ta Bayyana Farin Ciki da Kame Nnamdi Kanu, Ta Bayyana Dalili

Wata Kungiyar Igbo Ta Bayyana Farin Ciki da Kame Nnamdi Kanu, Ta Bayyana Dalili

  • Kungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze ta bayyana farin cikinta da kame Nnamdi Kanu na IPOB
  • Kungiyar ta ce wannan shine farkon karshen tashin tashina a yankin kudu maso gabashi
  • A yau ne aka sake kamo shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu bayan boyewa a wata kasa

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwode, kungiyar zamantakewar Ibo, ta ce kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB, zai kawar da yunkurin yakin basasa kuma ya kawo zaman lafiya a yankin kudu maso gabas, The Cable ta ruwaito.

A yau ne Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, an kame shugaban na IPOB bayan guduwan da ya yi zuwa wata kasar waje.

Da take magana a kan sake kame Nnamdi Kanu, Ohanaeze Ndigbo ta ce ci gaban zai kawo karshen tashin hankali a kudu maso gabas.

KARANTA WANNAN: Kabilar Ijaw Ta Gargadi Buhari Kan Tamkawa Tsagerun Neja Delta da Ya Yi

Wata Kungiyar Igbo Ta Bayyana Jin Dadinta da Kame Nnamdi Kanu, Ta Bayyana Dalili
Nnamdi Kanu, lokacin da aka kame shi | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A wata sanarwa daga Okechukwu Isiguzoro, babban sakataren kungiyar, kungiyar ta ce kin saurarar shawarar da shugabannin Ibo suka bashi ne ya kai shi ga halin da yake ciki yanzu.

Kungiyar ta shawarci gwamnatin tarayya da ta kula da shari’ar shugaban IPOB din a hankali domin kiyaye tashin hankali daga mabiyansa.

Wani yankin sanarwar ya ce:

“Sake kamo Nnamdi Kanu shugaban IPOB shine farkon karshen tashin hankali a yankin kudu maso gabashin Najeriya kuma darasi ne ga wasu cewa, kaucewa tashin hankali da kuma zubar da jinin marasa laifi na matasan Ibo ya saba da abinda aka san Ibo dashi, kuma son kai bai kamata a yi amfani da shi ba wajen neman arziki da neman suna ba."

Kungiyar ta yi kira da a kwantar da hankula sannan ta gargadi 'yan kabilar ta Ibo da su guji duk wani nau'i na zanga-zanga da jerin gwanon da zai kawo “karin masifa” ga yankin kudu maso gabas.

An gurfanar da Kanu a gaban Binta Nyako, wacce ta yanke hukuncin cewa a ci gaba da tsare shi a ofishin jami’an tsaro na farin kaya (DSS) har zuwa ranar 26 ga watan Yuli.

Dalilin da Yasa Na Gudu, Nnamdi Kanu Yayi Jawabi a Gaban Kotu

Shugaban ƙungiyar yan taware IPOB, Nnamdi Kanu, ya bayyana dalilin da yasa ya fice daga Najeriya bayan an bada belinshi a shekarar 2017, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Yace ya ɗauki matakin guduwa ne saboda an zagaye gidansa amma duk da haka saida ya samu nasarar ficewa.

Kanu ya ƙara da cewa idan bai tsere ba, to za'a iya kashe shi kamar yadda ake yiwa sauran mambobin ƙungiyar IPOB.

KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Majalisar Wakilai Ta Tabbatar da Nadin Manjo Faruk Yahaya

Muhimman Abubuwa 6 da Ya Kamata Ku Sani Game da Nnamdi Kanu Shugaban IPOB

A wani labarin, A yau ne rahotanni suka bayyana cewa, an kame shugaban kungiyar tsageru masu fafutukar ballewa daga Najeriya na IPOB, Nnamdi Kanu.

Masu bibiyar Legit.ng Hausa za su so sanin wanene wannan Nnamdi Kanu da aka kame har ake ta cece-kuce akansa.

Wannan yasa, muka tattaro bayanai masu muhimmanci game da Nnamdi Kanu domin mai karatu ya san wanene shugaban na IPOB.

Asali: Legit.ng

Online view pixel