Da Dumi-Dumi: Majalisar Wakilai Ta Tabbatar da Nadin Manjo Faruk Yahaya

Da Dumi-Dumi: Majalisar Wakilai Ta Tabbatar da Nadin Manjo Faruk Yahaya

  • Majalisar wakilai ta amince da nadin Janar Faruk Yahaya a matsayin shugaban hafsun sojoji
  • A makon da ya gabata ne majalisar wattijai ta tabbatar da nadin na Faruk Yahaya bayan bincike
  • An nada Faruk Yahaya ne bayan da tsohon COAS ya mutu a hadarin jirgin sama a jihar Kaduna

Majalisar wakilai ta tabbatar da Faruk Yahaya a matsayin shugaban hafsan soji (COAS).

Majalisar dokokin ta tabbatar da shi bayan gabatar da rahoto daga Babajimi Benson, shugaban kwamitin tsaro, The Cable ta ruwaito.

Idan baku manta ba, majalisar dattijai a ranar Talatar da ta gabata ne ta tabbatar da Yahaya a matsayin COAS.

Legit.ng Hausa ta gano cewa, yayin gabatar da rahoton, Benson ya ce Yahaya ya cika dukkan bukatun da ake fata daga gare shi.

Ya ce shugaban sojojin ya amsa duk tambayoyin da kwamitin ya yi masa yayin bincike"yadda ya dace".

KARANTA WANNAN: Tsadar Abinci: CBN Ta Gano Mafita Kan Tsadar Masara, Za Ta Tallafawa 'Yan Kasa

Da Dumi-Dumi: Majalisar Wakilai Ta Tabbatar da Nadin Manjo Faruk Yahaya
Manjo Janar Faruk Yahaya | Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Kwamitin ya binciki Yahaya makonni biyu da suka gabata, bayan da Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar, ya karanta wata wasika daga Shugaba Muhammadu Buhari dake neman a tabbatar da shi.

A yayin tantance shi, Yahaya ya ce ya halarci yaki da kuma aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Laberiya, ya kara da cewa tare da gogewarsa, zai iya tabbatar da ingantaccen tsaro a kasar.

'Yan majalisar baki daya sun amince da tabbatar da Yahaya a ranar Talata bayan da Idris Wase, mataimakin kakakin majalisar, ya gabatar da nadin nasa.

An nada Yahaya a ranar 27 ga Mayu don maye gurbin Ibrahim Attahiru wanda ya mutu a hatsarin jirgin saman soja tare da wasu jami’ai 10.

Majalisa ta tabbatar da Yahaya Farouk a matsayin COAS

Majalisar dattawar Nigeria, a ranar Talata ta tabbatar da nadin Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojojin kasa na Nigeria, The Punch ta ruwaito.

Vanguard ta ruwaito cewa majalisar ta cimma wannan matsayar ne bayan duba rahoton kwamitin hadaka kan tsaro karkashin jagorancin Sanata Aliyu Wamakko da Ali Ndume.

A ranar 2 ga watan Yuni ne shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar bukatarsa na neman amincewarsu game da tabbatar da nadin Yahaya.

An dora wa kwamitin tsaron karkashin jagorancin Wamakko nauyin tantance sabon babban hafsan sojojin kasar.

KARANTA WANNAN:

Babban Hafsan Sojoji Ya Kai Ziyara Imo, Ya Ce a Ragargaji IPOB Ba Sassautawa

A wani labarin, Faruk Yahaya, babban hafsan sojojin Najeriya, ya nemi sojojin da aka tura jihar Imo da su rubanya kokarinsu a yaki da haramtacciyar kungiyar IPOB a yankin kudu maso gabas, The Cable ta ruwaito.

Babban hafsan sojojin wanda ya yi kiran yayin da ya ziyarci sojojin ya ce ya zo jihar ne domin a tantance yanayin tsaro yadda yake a jihar.

An kai jerin hare-hare a jihar Imo a makonnin da suka gabata, ciki har da kisan wani jigon jam'iyyar APC, Ahmed Gulak.

Asali: Legit.ng

Online view pixel