Da dumi-dumi: PDP ta sake rashi na wasu sanatoci 3, sun koma APC

Da dumi-dumi: PDP ta sake rashi na wasu sanatoci 3, sun koma APC

  • Wasu sanatoci a karkashin jam'iyyar PDP sun sanar da sauya shekarsu zuwa APC a hukumance
  • Shugaban majalisar dattawa, Lawan Ahmed ne ya karanto wasikar da suka aika zauren a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni
  • Sanatocin sun hada da Sahabi Alhaji Yau mai wakiltar Zamfara ta Arewa, Lawali Hassan Anka mai wakiltar yankin Zamfara ta yamma da Peter Nwaoboshi mai wakiltar Delta ta Arewa

Sanatocin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) uku sun aike da wasiku zuwa ga shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan inda suke sanar da sauya shekarsu zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Sanata Lawan ya karanta wasikun a zauren majalisar a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni yayin zaman majalisar.

KU KARANTA KUMA: Wani Jigon Jam'iyyar PDP Ya Buƙaci INEC Ta Dakatar da Sauya Sheƙar Gwamnoni Zuwa APC

Da dumi-dumi: PDP ta sake rashi na wasu sanatoci 3, sun koma APC
Daya daga cikin sanatocin da suka sauya sheka Hoto: en Peter Nwaoboshi
Asali: Facebook

'Yan majalisar tarayyar su ne Sanata Sahabi Alhaji Yau (Sanata mai wakiltar Zamfara ta Arewa), Sanata Lawali Hassan Anka (Sanata mai wakiltar yankin Zamfara ta yamma), Sanata Peter Nwaoboshi (Sanata mai wakiltar Delta ta Arewa).

Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buhari Sallau ne ya wallafa batun sauya shekar nasu a shafinsa na zumunta ta Facebook.

Ya wallafa a shafin nasa:

"Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya karanta wasikun sanatoci uku da ke sanar da ficewarsu daga PDP zuwa APC.
"Su ne Sanata Sahabi Alhaji Yau (Yankin Zamfara ta Arewa), Sanata Lawali Hassan Anka (Yankin Zamfara ta Yamma) da Kuma Sanata Peter Nwaoboshi (Yankin Delta ta Arewa)."

KU KARANTA KUMA: An rantsar da kuliyar da ta daure tsoffin gwamnonin Najeriya 2 a matsayin mai shari’a a kotun daukaka kara

PDP ta rasa mambobinta 2 a majalisar wakilai, sun sauya sheka zuwa APC

A gefe guda, mun ji a baya cewa mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar wakilai sun nuna adawa ga sauya shekar wasu mambobin jam’iyyar zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, a ranar Talata, 29 ga watan Yuni.

Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Toby Okechukwu, da wasu sun yi adawa da sauya shekar wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Cross Ribas, Lego Idagbo da Michael Etiaba, wanda aka sanar yayin zaman majalisar na yau Talata.

Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da sauya shekar a zaman majalisar inda ya ce 'yan majalisar biyu sun fice daga PDP sun koma APC, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel