Da dumi-dumi: PDP ta rasa mambobinta 2 a majalisar wakilai, sun sauya sheka zuwa APC

Da dumi-dumi: PDP ta rasa mambobinta 2 a majalisar wakilai, sun sauya sheka zuwa APC

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta rasa mambobinta biyu a majalisar wakilai ta tarayya
  • 'Yan majalisar daga jihar Cross Ribas, Lego Idagbo da Michael Etiaba sun sauya sheka zuwa APC a ranar Talata, 29 ga watan Yuni
  • Sun bayyana rikice-rikicen da ke faruwa a PDP a jihar su a matsayin dalilin ficewar su

Mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar wakilai sun nuna adawa ga sauya shekar wasu mambobin jam’iyyar zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, a ranar Talata, 29 ga watan Yuni.

Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Toby Okechukwu, da wasu sun yi adawa da sauya shekar wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Cross Ribas, Lego Idagbo da Michael Etiaba, wanda aka sanar yayin zaman majalisar na yau Talata.

KU KARANTA KUMA: An rantsar da kuliyar da ta daure tsoffin gwamnonin Najeriya 2 a matsayin mai shari’a a kotun daukaka kara

Da dumi-dumi: PDP ta rasa mambobinta 2 a majalisar wakilai, sun sauya sheka zuwa APC
Sun bayyana rikice-rikicen da ke faruwa a PDP a jihar su a matsayin dalilin ficewar su Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da sauya shekar a zaman majalisar inda ya ce 'yan majalisar biyu sun fice daga PDP sun koma APC, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Dukansu sun bayyana rikice-rikicen da ke faruwa a PDP a jihar su a matsayin dalilin ficewar su, jaridar The Cable ta ruwaito.

Sai dai kuma, mambobin na PDP sun ce sauya shekarsu ya saba wa doka.

Okechukwu ya bayyana cewa majalisar ta kara wasu jerin karya doka ta hanyar karbar sauya shekar nasu.

KU KARANTA KUMA: Tsohuwar rasit ta nuna ‘yan siyasa na biyan kudi kafin su zama mambobin jam’iyya a baya

Gbajabiamila, ya yi ikirarin cewa mambobin PDP ba su da ikon tantance yanayin sauya shekarsu, yana mai cewa kotu ce kawai za ta iya yin hakan.

PDP na cikin matsala yayinda Sanatan Zamfara ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar

A gefe guda, Sanata mai wakiltar yankin Zamfara ta Tsakiya a majalisar dokoki ta kasa, Sanata Hassan Mohammed Nasiha, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP.

Dan majalisar ya sanar da sauya shekarsa a cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata, 29 ga watan Yuni, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce ya shawararsa ta ficewa daga PDP ya zama dole saboda rugujewar dimokiradiyyar cikin gida da rabuwar kan PDP a jihar ta Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel