An rantsar da kuliyar da ta daure tsoffin gwamnonin Najeriya 2 a matsayin mai shari’a a kotun daukaka kara

An rantsar da kuliyar da ta daure tsoffin gwamnonin Najeriya 2 a matsayin mai shari’a a kotun daukaka kara

  • Akalla alkalai 18 ne aka kara wa girma zuwa kotun daukaka kara a wani bikin da aka yi a Abuja
  • Mai shari'a Adebukola Banjoko na daga cikin alkalan da aka amince da daukaka matsayinsu zuwa Kotun daukaka kara
  • Banjoko ce ta yankewa tsohon gwamna, Joshua Dariye na jihar Filato da Jolly Nyame na jihar Taraba hukunci da kuma daure su

Babban Alkalin Najeriya (CJN), Mai shari’a Ibrahim Muhammad a ranar Litinin, 28 ga Yuni, ya rantsar da Mai Shari’a Adebukola Banjoko ta Babbar Kotun Birnin Tarayya zuwa ofishin Alkalin Kotun daukaka kara.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa mai shari'a Banjoko ce ta yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame hukuncin shekaru 14 a gidan yari kan tuhumar cin hanci ba tare da zabin biyan tara ba.

KU KARANTA KUMA: Guguwar sauyin sheka: APC ta fara tattaunawa da wasu gwamnonin PDP 3, jam’iyyar adawa ta yi martani

An rantsar da kuliyar da ta daure tsoffin gwamnonin Najeriya 2 a matsayin mai shari’a a kotun daukaka kara
Babban alkalin Najeriya, Justis Tanko Mohammed a wajen bikin rantsar da alkalan kotun daukaka kara 18 Hoto: @RtHonAhmedwase
Asali: Facebook

Ta kuma gurfanar da Joshua Dariye, tsohon gwamnan jihar Filato, kuma ta yanke masa hukuncin shekaru 14 a kurkuku, jaridar Sun News ta ruwaito.

Cikakken jerin sabbin alkalan ya nuna cewa alkalai 11 daga cikin 18 sun fito ne daga yankin arewa yayin da ragowar bakwai suka fito daga yankin kudu.

An nada Alkalan Shari'a 34 a jihar Kano bayan gwaji

A bangare guda, da amincewar Mai Shari’a Nura Sagir, babban alkalin Kano, an kara wasu alkalai 34 na kotun shari’ar Musulunci a jihar a ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni.

Kakakin ma’aikatar shari’ar jihar, Baba Jibo-Ibrahim ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, jaridar Punch ta ruwaito.

Jibo-Ibrahim a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa Babban Alkalin ya amince da nadin alkalan ne bayan sun ci jarabawar da Hukumar Kula Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC) ta gudanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel