Rahotanni Sun Bayyana Yadda Aka Kamo Nnamdi Kanu a Wata Kasar Turai

Rahotanni Sun Bayyana Yadda Aka Kamo Nnamdi Kanu a Wata Kasar Turai

  • Rahotanni sun bayyana yadda aka kamo shugaban haramtacciyar kungiyar nan ta tsagerun IPOB
  • Rahotanni sun ce, an kame shugaban na IPOB a kasar Turai, in da aka yaudareshi da karbar makamai
  • An ce, ya bar kasar Ingila zuwa Crech domin ya gana da masu bashi kyautar makamai ga kungiyar IPOB

Wani rahoto na jaridar Daily Sun ya nuna cewa an kama Mazi Nnamdi Kanu a Jamhuriyar Czech.

A cewar rahoton, shugaban IPOB ya yi tafiya daga kasar Ingila zuwa Singapore saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba kafin ya tafi Jamhuriyar Czech a ranar Juma’ar da ta gabata, 25 ga Yuni.

Rahoton ya ambato wata majiya, inda ya ce akwai wani bayani da jami'an Jamhuriyar Czech suka ba gwamnatin Najeriya, wanda ya kai ga kame Kanu a birnin Prague.

KARANTA WANNAN: Muhimman Abubuwa 6 da Ya Kamata Ku Sani Game da Nnamdi Kanu Shugaban IPOB

Rahoto ya bayyana yadda aka kamo Nnamdi Kanu a wata kasar Turai
Shugaban kungiyar ta'addanci ta IPOB, Nnamdi Kanu | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Hakazalika, P.M News ta ruwaito cewa an kama Kanu ne a Jamhuriyar Czech inda aka yaudare shi zuwa kasar don karbar kyautar makamai ga kungiyar tsaron IPOB wato ESN.

Kanu dan Burtaniya ne kuma yana da fasfo din kasar Ingila. Don zuwa Jamhuriyar Czech, wadanda ke da fasfo din Burtaniya ba sa bukatar biza.

Kuma yana daukar kasa da awanni biyu ne kacal daga Ingila zuwa Prague, babban birni Jamhuriyar Czech.

Duk da wadannan rahotanni, hukumomin Najeriya ba su ce uffan ba kan yadda aka kama Kanu.

Ingila ta tabbatar da kamun Kanu, ta ce ba a kasar ta aka kame shi ba

A baya Legit.ng ta rahoto a baya cewa hukumar Ingila tayi martani game da kamun da aka yi wa Kanu.

Dean Hurlock, mai magana da yawun Babban Kwamitin na Burtaniya, ya shaida wa wata jaridar Najeriya cewa yayin da za su iya tabbatar da kamun na Kanu, amma ba a kama shi a Burtaniya ba.

KARANTA WANNAN: Bayan Najeriya, An Shigar da Karar Twitter a India Kan Yunkurin Cutar da Kasar

Wata Kungiyar Igbo Ta Bayyana Farin Ciki da Kame Nnamdi Kanu, Ta Bayyana Dalili

A wani labarin, Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwode, kungiyar zamantakewar Ibo, ta ce kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB, zai kawar da yunkurin yakin basasa kuma ya kawo zaman lafiya a yankin kudu maso gabas, The Cable ta ruwaito.

A yau ne Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, an kame shugaban na IPOB bayan guduwan da ya yi zuwa wata kasar waje. D

a take magana a kan sake kame Nnamdi Kanu, Ohanaeze Ndigbo ta ce ci gaban zai kawo karshen tashin hankali a kudu maso gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.