Abun Mamaki: Wani Fursuna Ya Yi Digirin Digirgir a Fannin Sadarwa a Gidan Yari
- Wani fursuna dake zaman gidan gyaran hali a jihar Anambra ya kammala karatun digirin digirgir
- Jude Onwuzulike, ya karɓi takardun shaidar kammala karatun digirinsa na biyu daga jami'ar NOUN
- Daraktan jami'ar NOUN, reshen Anambra tace ba dan ɗalibin na gidan yari ba da dashi za'a yi bikin yaye ɗalibai a Abuja
Wani fursuna a gidan gyaran halin Awka, jihar Anambra, Jude Onwuzulike, ya karɓi sakamako kala biyu daga jami'an NOUN lokacin da yake zaman gidan yarinsa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Jigon PDP Ya Caccaki El-Rufa'i, Ya Buƙaci Ya Sadaukar da Albashinsa Ga Ɗalibai
Onwuzulike, ya karɓi sakamakon karatun difloma ta gaba da digiri (PGD) da kuma takardar kammala digirin digirgir.
An kirkiro shirin ne domin fursunoni
Da yake jawabi yayin miƙa takardun sakamakon, rajistaran jami'ar NOUN, Felix Edoka, yace an samar da wannan shirin ne domin taimakawa rayuwar mutane, da ya haɗa da koyar da fursunoni ilimin zamani.
Edoka, wanda mataimakinsa, Oladipo Ajayi, ya wakilta ya yaba wa wanda ya samu wannan nasara duk kuwa da kasancewar sa a gidan gyaran hali.
Da take nata jawabin, Daraktan jami'an NOUN, reshen Anambra, Scholastica Ezeribe, ta bayyana cewa wannan shirin koyarwa ta yanar gizo yana nuna muhimmancin ilima har ga yan gidan yari.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Dalilin da Yasa Na Gudu, Nnamdi Kanu Yayi Jawabi a Gaban Kotu
An baiwa Onwuzulike takardar sakamako guda biyu
Da take tabbatar da ingancin takardun sakamakon ɗalibin, Ezeribe, ta bayyana cewa ɗalibin ya tsallake duk wani siraɗi da aka sanya masa a lokacin gudanar da karatunsa ta yanar gizo.
Tace: "Zamu iya miƙa mishi takardunsa a lokacin bikin yaye ɗaliban mu a Abuja, amma saboda yanayin da yake ciki na zaman gidan yari, shine yasa muka kawo mishi takardun sa guda biyu har inda yake."
A wani labarin kuma FG Ta Faɗi Ranar da Zata Kulle Layukan Wayar da Ba'a Haɗasu da NIN Ba
Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar da zata fara kulle duk wani layin waya da ba'a haɗa shi da lambar zama ɗan ƙasa NIN ba.
Gwamnatin ta faɗi haka ne a wani jawabi da hukumar sadarwa NCC tare da hukumar NIMC suka fitar, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Asali: Legit.ng