Sakataren PDP, Nakusa da Bukola Saraki, Olatunji, Ya Fice Daga Jam'iyyar

Sakataren PDP, Nakusa da Bukola Saraki, Olatunji, Ya Fice Daga Jam'iyyar

  • Sakataren shirye-shirye na jam'iyyar PDP a jihar Kwara ya miƙa takardar yin murabus daga jam'iyyar
  • Mallam Olatunji Buhari, yace ya ɗauki wannan matakin ne domin samun damar kulawa da iyalinsa da kasuwancinsa
  • Amma wata majiya ta kusa da jigon siyasar ta bayyana cewa bada jimawa ba zai faɗi inda ya dosa a siyasance

Sakataren shirye-shirye na jam'iyyar PDP reshen jihar Kwara, Mallam Sulyman Olatunji Buhari, wanda nakusa ne da tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, yayi murabus daga jam'iyyar, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wani Gwamna Ya Kori Ma'aikata da Dama a Jiharsa, Ya Tilasta Wa Wasu Yin Ritaya

Takardar murabus ɗin da Buhari ya aike da adireshin shugaban PDP na jihar, Hon Kola Shittu, tana ɗauke da kwanan watan 28 ga watan Yuni 2021.

A jawabin da ya rubuta a wasiƙar, Buhari ya bayyana cewa wasu dalilan kai-da-kai ne suka saka shi aje muƙaminsa.

Sakataren shirye-shirye na PDP jihar Kwara yayi Murabus
Sakataren PDP Kuma Nakusa da Bukola Saraki, Olatunji, Ya Miƙa Takardar Murabus Daga Jam'iyyar Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Legit.ng hausa ta gano cewa ɗan siyasar ya ɗauki wannan matakin ne saboda canjin wurin zama da yayi zuwa Abuja.

Wani ɓangaren takardar murabus ɗin tace:

"Ina mai farin cikin shaida muku matakin dana ɗauka na yin murabus daga muƙamin sakataren tsara shirye-shirye na jam'iyyar PDP reshen jihar Kwara."

"Na ɗauki wannan matakin ne domin in samu damar kulawa da iyalina da kuma kasuwanci na. Ina miƙa godiya ta ga shugabannin wannan jam'iyyar saboda irin damar da suka bani na riƙe muƙamai da dama a wasu shekaru da suka gabata."

KARANTA ANAN: Bayan Matawalle, Jam'iyyar PDP Ta Faɗi Babban Dalilin da Yasa Gwamnoni Ke Ficewa Daga Cikinta

Buhari ya taɓa riƙe shugaban CPC

Mallam Buhari ya kasance shugaban jam'iyyar CPC a shekarar 2011 lokacin da gwamna mai ci yanzun, AbdulRahaman AbdulRazaq, shine ɗan takarar gwamna a jam'iyyar.

Wata majiya tace bada jimawa ba, Mallam Buhari, zai bayyana matakin da ya ɗauka a siyasance kan inda zai dosa.

A wani labarin kuma APC Ta Shirya Babban Gangami Yayin da Jiga-Jiganta Zasu Dira Jihar Zamfara

Jam'iyyar APC ta shirya babban gangami na musamman ranar Talata domin tarbar gwamnan Zamfara, Matawalle, kamar yadda punch ta ruwaito.

Ana sa ran jiga-jigan jam'iyyar na ƙasa da na jihar Zamfara ne zasu tarbi gwamnan tare da yan majlisar dokokinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel