APC Ta Shirya Babban Gangami Yayin da Jiga-Jiganta Zasu Dira Jihar Zamfara

APC Ta Shirya Babban Gangami Yayin da Jiga-Jiganta Zasu Dira Jihar Zamfara

  • Jam'iyyar APC ta shirya babban gangami na musamman ranar Talata domin tarbar gwamnan Zamfara, Matawalle
  • Ana sa ran jiga-jigan jam'iyyar na ƙasa da na jihar Zamfara ne zasu tarbi gwamnan tare da yan majlisar dokokinsa
  • Mataimakin gwamna, Bar. Mahdi Aliyu da wasu ƙalilan daga cikin ma'aikata basu amince da sauya shekar ba

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, zai tabbatar da komawarsa jam'iyyar APC a ranar Talata.

Saboda haka ne jam'iyyar ta shirya wani babban gangami na tarbar gwamna Matawalle zuwa APC wanda zai gudana a Trade Fair dake Gusau, babban birnin Zamfara da misalin ƙarfe 10 na safe, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Na Gode Wa Allah da Gwamna Matawalle Ya Amsa Kira na Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC, Tsohon Kwamishina

Ana sa ran jiga-jigan jam'iyyar APC na ƙasa da na jihar Zamfara ne zasu karɓi gwamnan, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Alhaji Ibrahim Dosara, yace ana sa ran aƙalla gwamnoni 18 ne zasu dira jihar Zamfara domin tarbar gwamna Matawalle.

Yace: "Gwamnonin APC ƙaraƙashin jagorancin shugaban kwamitin riƙo na jam'iyyar, Gwamna Mai Mala Buni, sune zasu tarbi Matawalle."

APC ta shirya Gangami na musamman Domin Matawalle
APC Ta Shirya Babban Gangami Yayin da Jiga-Jiganta Zasu Dira Jihar Zamfara Hoto: vangaurdngr.com
Asali: UGC

Matawalle ya samu matsala da gwamnonin kudu na PDP

Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Matawalle ya daɗe yana shirin komawa APC tun bayan lokacin da takwarorinsa na kudancin ƙasar nan suka fara zarginsa kan yadda yake tafiyar da haƙar ma'adanan ƙasa dake jihar.

Gwamnan ya ƙara harzuƙa lokacin da gwamnonin jam'iyyar PDP daga yankin kudancin ƙasar nan suka soki tsarin shi na siyarda ma'adanai ga babban bankin Najeriya (CBN).

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Hankalin Mutane Ya Tashi Yayin da Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba da Ɗiyar Wani Ɗan Fulani

Yan majalisar dokoki baki ɗaya zasu mara wa gwamna baya

Gwamna Matawalle zai koma jam'iyyar APC tare da baki ɗaya yan majalisar dokokin jiharsa in banda Kabiru Mafara, mai wakiltar mazaɓar Anka/Mafara.

Hakazalika, Mataimakin gwamna, Bar. Mahdi Aliyu, tare da wasu jami'an gwamnatin jihar zasu cigaba da kasancewa a PDP.

A wani labarin kuma Babu Wanɗanda Suka Dace da Mulkin Najeriya a 2023 Fiye da Tinubu/Ganduje, Inji TPN

Shugaban ƙungiyar magoya bayan Tinubu (TPN) reshen jihar Kano, Muhammad Tajo, yace babu kamar Tinubu a 2023.

Tajo ya yi kira ga gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da ya amince ya nemi mataimakin shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel