Bayan Matawalle, Jam'iyyar PDP Ta Faɗi Babban Dalilin da Yasa Gwamnoni Ke Ficewa Daga Cikinta
- Wani jigon babban jam'iyyar hamayya PDP ya bayyana ainihin dalilin da yasa gwamnoni ke guduwa daga jam'iyyar
- A cewarsa duk gwamnan da ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC to ba shi da dalilin yin hakan
- Sai-dai PDP ta zargi wasu daga cikin yan APC da yi musu maƙarƙashiya da tilastawa gwamnonin sauya sheƙa
Wani jigo kuma babba daga cikin yan majalisar zartarwa a jam'iyyar PDP yace jam'iyyarsu ba zata iya cewa komai ba dangane da sauya sheƙar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, kamar yadda leadership ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Wata Sabuwa: Obasanjo Ya Sake Yin Magana a Kan Jita-Jitar An Sauya Buhari da Jibrin Sudan
Yace jam'iyyar PDP ba ta da ikon da zata hana gwamnan komawa jam'iyya mai mulki wato APC
Sai-dai ya ƙara da cewa Matawalle bai faɗawa PDP dalilinsa na ficewa daga cikinta ba, amma akwai wasu daga cikin yan APC dake matsawa gwamnoni su sauya sheƙa.
Jigon a PDP yace: "Matsayar mu itace ba zamu ce komai ba gane da ficewarsa, kuma ba zamu ɗauki wani mataki a kan haka ba."
"Har zuwa yanzun gwamnan bai faɗa mana dalili da yasa ya fice daga jam'iyyar mu ba, kuma baida wani dalili na cewa an mishi ba dai-dai ba."
Gwamnonin basu da hujjar ficewa daga PDP
Ya cigaba da cewa: "Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers, wanda ya koma APC, har yanzun bai faɗa mana abinda PDP ta masa wanda ba dai-dai ba."
"Hakazalika, gwamna Dev Umahi na jihar Ebonyi, da yake ta kuka cewa ana rashin adalci a PDP, har yanzun ya gaza amsa mana tambayar mu cewa a ina ake rashin adalcin."
KARANTA ANAN: Ba Gudu Ba Ja da Baya a Matakin Mu Na Korar Ma'aikata, El- Rufa'i Ya Faɗawa Buhari
Babban jigon PDP ɗin yace akwai wasu mutane a cikin jam'iyyar APC dake jan hankalin gwamnonin na su koma jam'iyyar su.
A cewarsa, duk wanda ya yanke cewa zai fice daga jam'iyyar mu, bamu da ikon hana shi.
A wani labarin kuma APC Ta Shirya Babban Gangami Yayin da Jiga-Jiganta Zasu Dira Jihar Zamfara
Jam'iyyar APC ta shirya babban gangami na musamman ranar Talata domin tarbar gwamnan Zamfara, Matawalle, kamar yadda punch ta ruwaito.
Ana sa ran jiga-jigan jam'iyyar na ƙasa da na jihar Zamfara ne zasu tarbi gwamnan tare da yan majlisar dokokinsa.
Asali: Legit.ng