Tsohuwar rasit ta nuna ‘yan siyasa na biyan kudi kafin su zama mambobin jam’iyya a baya

Tsohuwar rasit ta nuna ‘yan siyasa na biyan kudi kafin su zama mambobin jam’iyya a baya

  • Wata tsohuwar rasit da wani dan jam’iyyar Action Group, Raimi Ajani, ya biya silalla daya don shiga jam'iyyar a 1951 ya bayyana a shafukan sada zumunta
  • A da, mambobin jam’iyya suna biyan kudi don shiga jam’iyyun siyasa sabanin yanzu da rajista ta kasance kyauta
  • Kuma an ce cin hanci da rashawa bai yawaita ba a lokacin
  • Ayo Ojeniyi ne ya wallafa rasit din a Facebook kuma 'yan Najeriya ba su yi kasa a gwiwa ba wajeen cike sashen sharhi da tunaninsu

Wata tsohuwar takardar rasit da ta bayyana kwanan nan a shafukan sada zumunta ta tabbatar da cewa a da rijistar shiga jam’iyyun siyasa ba kyauta bane.

Rasitin da wani dan Najeriya mai suna Ayo Ojeniyi ya wallafa ya kasance na jam’iyyar Action Group wacce aka baiwa Raimi Ajani bayan ya biya silalla daya don shiga jam'iyyar a 1951.

KU KARANTA KUMA: Guguwar sauyin sheka: APC ta fara tattaunawa da wasu gwamnonin PDP 3, jam’iyyar adawa ta yi marta

Tsohuwar rasit ta nuna ‘yan siyasa na biyan kudi kafin su zama mambobin jam’iyya a baya
Raimi Ajani, ya biya silalla daya don shiga jam'iyyar Action Group Hoto: Ayo Ojeniyi
Asali: Facebook

A cewar Ojeniyi, an yi amfani da kudaden da mambobin suka biya wajen tafiyar da jam’iyyar. Ya ce cin hanci da rashawa bai yi kamari ba a lokacin saboda mutane na tsoron a kama su.

Da yake wallafa rasitin, Ojeniyi ya rubuta:

"A wancan zamanin, membobin jam'iyya suna biyan kudin rajista don tafiyar da jam'iyyar !!! Cin hanci da rashawa haramun ne kuma bai yawaita ba. Tsoron kada a kama mutum ya hana cin hanci da rashawa. Mutane koyaushe suna kare martaban sunan gidansu !!!
"Anan wannan mutumin Raimi Ajani ya biya silalla daya don shiga jam’iyyar Action Group a watan Satumban 1951."

KU KARANTA KUMA: An rantsar da kuliyar da ta daure tsoffin gwamnonin Najeriya 2 a matsayin mai shari’a a kotun daukaka kara

Mutane da dama sun yi martani a kan tsohuwar rasit din

Sharafa Ololade ta ce:

"Afenifere guda dai da wasu ‘Yan Yarbawa ke kira sunaye yanzu, kawai saboda sabani na siyasa ???"

Akinlawon Akintunde ya yi tsokaci:

"Kenan ana iya gargadin shugaban jam'iyyar, a ba shi shawarar ya sauka sannan kuma ana iya yiwa zababbun membobin kiranye.
"’Yan Afenifere na siyasar yau sun sayar da lamiri, martaba da mutuncinsu cewa ba za su iya daukaka darajar jam'iyya ba amma a maimakon haka suna karbar umarnin kan lamuran jam'iyyar kawai daga Abuja."

Clement Adenugba ya rubuta:

"Har yanzu ina da katin rajistana na UPN wanda da shi nake biyan kudin dan jam’iyya a shekarar 1979."

Adeyemo Olabintan Abu Mu'az ya ce:

"'Yan siyasan zamani sun barnatar da komai. Waɗannan kyawawan ranaku sun shuɗe."

A wani labarin, tsohon kwamishinan raya karkara a jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Abdullahi Tsafe, yace gwamna Bello Matawalle ya sauya sheƙa zuwa APC.

A jawabin da tsohon kwmishinan ya fitar, wanda aka aike wa legit.ng ranar Lahadi 27 ga watan Yuni, yace gwamna Matawalle zai tabbatar da sauya shekarsa a hukumance ranar Talata.

Tsafe, wanda ɗaya ne daga cikin jiga-jigan APC a Zamfara, shi ne mutum na farko da ya fara kiran gwamna Matawalle ya dawo APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng