Guguwar sauyin sheka: APC ta fara tattaunawa da wasu gwamnonin PDP 3, jam’iyyar adawa ta yi martani

Guguwar sauyin sheka: APC ta fara tattaunawa da wasu gwamnonin PDP 3, jam’iyyar adawa ta yi martani

  • Wasu karin gwamnonin PDP uku na iya komawa jam'iyyar APC mai mulki gabanin zabukan 2023 kamar yadda ake zargin an fara tattaunawa da su
  • Gwamnonin sune Okezie Ikpeazu na jihar Abia, Ifeanyi Ugwanyi na jihar Enugu da Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa
  • Sai dai, PDP ta yi watsi da tattaunawar sauya shekar da ake zargin ana yi, ta shigar da kara don dakatar da yunkurin gwamnan Zamfara na komawa APC

Ana zargin cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara tattaunawa da gwamnonin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) guda uku da niyyar dawo da su jam'iyyar mai mulki.

A cewar jaridar The Punch, kwamitin riko na kasa na jam’iyyar karkashin jagorancin Mai Mala Buni ya fara tattaunawa da gwamnonin PDP uku wadanda suka hada da: Okezie Ikpeazu na jihar Abia, Ifeanyi Ugwanyi na jihar Enugu da Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.

KU KARANTA KUMA: Wani Tsohon Kwamishina Ya Sha da Ƙyar Yayin da Yan Bindiga Suka Buɗe Wa Tawagar Motocinsa Wuta

Guguwar sauyin sheka: APC ta fara tattaunawa da wasu gwamnonin PDP 3, jam’iyyar adawa ta yi martani
APC ta fara tattaunawa da wasu gwamnonin PDP 3 da nufin dawo da su cikinta Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Jaridar ta ambato wani babban mamba a jam’iyya mai mulki yana tabbatar da hakan.

Legit.ng ta tattaro cewa majiyar ta kuma bayyana cewa tuni an kammala batun sauya shekar Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Zancen sauya shekar Ikpeazu yana a matakin ci gaba

Majiyar ta APC ta ce Gwamna Ikpeazu na jihar Abia ne zai zama na gaba da zai shiga jam’iyya mai mulki, inda ta kara da cewa tattaunawar ta kai wani mataki na ci gaba.

Ya ce sauran gwamnonin biyu ma sun aika da wakilai kuma tattaunawa na ci gaba. A cewar majiyar da ba a bayyana sunanta ba, aikin da APC ta yi na sake rajistar mambobi an fadada su ne bisa dabaru don kwato gwamnonin PDP da masu biyayya gare su.

Kawo yanzu, gwamnonin PDP biyu, David Umahi na jihar Ebonyi da Ben Ayade na jihar Kuros Riba, sun koma APC a hukumance. Sanya ran Matawalle na Zamfara zai bi sahu a ranar Talata, 29 ga Yuni.

PDP ta mayar da martani, tayi watsi da tattaunawar sauya shekar

Da yake maida martani, kakakin PDP, Kola Ologbondiyan, ya yi watsi da shirin da ake zargin APC na yi, yana mai cewa jam’iyya mai mulki “ta rasa alkibla gaba daya”.

Kalaman nasa:

"Suna fatan ganin dukkan gwamnoninmu a tsakiyarsu saboda basa tabuka komai, amma 'yan Najeriya sun san banbancin kuma ba za'a iya yaudarar su ba."

APC Ta Shirya Babban Gangami Yayin da Jiga-Jiganta Zasu Dira Jihar Zamfara

A gefe guda, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, zai tabbatar da komawarsa jam'iyyar APC a ranar Talata.

Saboda haka ne jam'iyyar ta shirya wani babban gangami na tarbar gwamna Matawalle zuwa APC wanda zai gudana a Trade Fair dake Gusau, babban birnin Zamfara da misalin ƙarfe 10 na safe, kamar yadda punch ta ruwaito.

Ana sa ran jiga-jigan jam'iyyar APC na ƙasa da na jihar Zamfara ne zasu karɓi gwamnan, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel