Wani Tsohon Kwamishina Ya Sha da Ƙyar Yayin da Yan Bindiga Suka Buɗe Wa Motocinsa Wuta
- Tsohon kwamishina a jihar Ondo, Joseph Ikpea, ya sha da ƙyar a hannun masu garkuwa da mutane
- Rahoto ya bayyana cewa Ikpea yana cikin bacci wasu yan bindiga suka buɗe wa tawagar motocinsa wuta
- Shugaban matasan Esan ya roƙi gwamnati ta jawo jami'an tsaron sa kai a jikinta don magance matsalolin tsaro
Tsohon kwamishinan man fetur da gas a jihar Ondo, Joseph Ikpea, ya sha da ƙyar yayin da wasu yan bindiga suka kaiwa tawagar motocinsa hari ranar Lahadi a kan hanyar Igbanke/Agbor, kamar yadda punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Bayan Matawalle, Jam'iyyar PDP Ta Faɗi Babban Dalilin da Yasa Gwamnoni Ke Ficewa Daga Cikinta
Ikpea ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga mahaifarsa, Ewatta, inda ya halarci wani taro da aka karrama shi.
Yace: "Ina cikin bacci lokacin da lamarin ya faru, amma a cewar mai taimakamun na musamman da masu tsaro na, yan bindigan sun kai 10-12 sanye da baƙaƙen kaya, kuma sun saka riga mara jin harbi."
"Wani abun mamaki shine bayan haka sun kai hari madakatar yan sanda wacce babu kowa a wurin. Jami'an yan sandan sun dawo wurin yan mintuna ƙaɗan da faruwar lamarin."
KARANTA ANAN: Wata Sabuwa: Obasanjo Ya Sake Yin Magana a Kan Jita-Jitar An Sauya Buhari da Jibrin Sudan
Ya kamata gwamnati ta haɗa hannu da yan bijilanti
Shugaban ƙungiyar matasan Esan a jihar Ondo, Kingsley Ohens, ya shawarci gwamnatin jihar ta haɗa hannu da jami'an tsaron sa kai, yan bijilanti.
Ohens ya ƙara da cewa yan bijilanti na da rawar da zasu taka wajen magance matsalar masu garkuwa da yan bindiga.
A wani labarin kuma Ba Gudu Ba Ja da Baya a Matakin Mu Na Korar Ma'aikata, El- Rufa'i Ya Faɗawa Buhari
Gwamnan Kaduna, El-Rufa'i, ya shaida wa shugaba Buhari sabon kudirin da gwamnatinsa ta bullo da shi na yin gyara, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Gwamnan yace a halin yanzun an fara aikin ɗaukar ma'aikata 10,000 a jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng