Wata Sabuwa: Obasanjo Ya Sake Yin Magana a Kan Jita-Jitar An Sauya Buhari da Jibrin Sudan

Wata Sabuwa: Obasanjo Ya Sake Yin Magana a Kan Jita-Jitar An Sauya Buhari da Jibrin Sudan

  • Obasanjo ya sake maganan kan jita-jitar da aka yi a baya lokacin da Buhari ya daɗe a Landan neman Lafiya
  • Tsohon shugaban yace wannan rahoton da aka yaɗa a wancan lokacin babban abun dariya ne
  • Amma abun mamaki idan ka hau kafafen sada zumunta zakaga wasu mutane da dama sun yarda

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana jita-jitar da aka yi a baya cewa shugaba Buhari ya mutu kuma an maye gurbinsa da wani Jibril daga Sudan a matsayin abun dariya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ba Gudu Ba Ja da Baya a Matakin Mu Na Korar Ma'aikata, El- Rufa'i Ya Faɗawa Buhari

Da yake jawabi a wurin wani taron matasa a jihar Ogun ranar Lahadi, Obasanjo ya kira jita-jitar a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da yasa ake batanci ga kafafen sada zumunta.

Jita-jitar mutuwar shugaban ƙasa, wanda daga baya aka gano ƙarya ne kasancewar babu hujja, ana zargin shugaban yan tawaren IPOB da ƙirƙirarta.

Shugaba Buhari tare da Obasanjo
Wata Sabuwa: Obasanjo Ya Sake Yin Magana a Kan Jita-Jitar An Sauya Buhari da Jibrin Sudan Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Na yi imanin jita-jitar ƙarya ce

Tsohon shugaban yace a wancan lokacin akwai wanda ya tinkare shi ya tambaye shi shin ya yarda da rahoton.

Yace: "Wani yazo wajena da sa ransa, ya tambayeni shin na yarda da rahoton mutuwar shugaba da kuma maye gurbinsa da wani?"

"Nace masa kai ka amince da haka? Na faɗa masa taya Buhari zai mutu kuma mu bamu sani ba, har a ɗakko wani daga Sudan ya zauna kujerar Buhari."

KARANTA ANAN: NANS Ta Gana da Sheikh Gumi, Ta Buƙaci a Saƙo Ɗaliban da Aka Sace

"Wannan abun dariya ne matuƙa, amma idan kana amfani da kafar sada zumunta zakaga wasu mutane sun yarda da hakan. Kafafen sada zumunta suna da amfani amma suna jawa kansu zagi da cin mutunci."

A wani labarin kuma APC Ta Shirya Babban Gangami Yayin da Jiga-Jiganta Zasu Dira Jihar Zamfara

Jam'iyyar APC ta shirya babban gangami na musamman ranar Talata domin tarbar gwamnan Zamfara, Matawalle, kamar yadda punch ta ruwaito.

Ana sa ran jiga-jigan jam'iyyar na ƙasa da na jihar Zamfara ne zasu tarbi gwamnan tare da yan majlisar dokokinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262