Ba Gudu Ba Ja da Baya a Matakin Mu Na Korar Ma'aikata, El-Rufa'i Ya Faɗawa Buhari

Ba Gudu Ba Ja da Baya a Matakin Mu Na Korar Ma'aikata, El-Rufa'i Ya Faɗawa Buhari

  • Gwamnan Kaduna, El-Rufa'i, ya shaida wa shugaba Buhari sabon kudirin da gwamnatinsa ta bullo da shi na yin gyara
  • Gwamnan yace a halin yanzun an fara aikin ɗaukar ma'aikata 10,000 a jihar Kaduna
  • Yace gwamnatinsa ba zata aiwatar da wata yarjejeniya ba matuƙar ta saɓa wa kudirin da ta ɓullo da shi

Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya yiwa shugaban ƙasa Buhari cikakken bayani kan kudirin gwamnatinsa na yin garambawul da kuma matakan da ya ɗauka na aiwatarwa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: NANS Ta Gana da Sheikh Gumi, Ta Buƙaci a Saƙo Ɗaliban da Aka Sace

Gwamnan yace gwamnatinsa zata buƙaci bayani kan matakin da ƙungiyar kwadugo fa ɗauka, inda zata kafa hukumar da zata binciki yajin aikin NLC da zanga-zngar da ta gudanar a watan Mayu 2021.

El-Rufa'i ya kara da cewa ya tabbatarwa shugaba Buhari cewa, gwamnatinsa ba zata sake bari a maimaita halin da mutanen jihar suka shiga na ƙunci, matsin tattalin arziƙi da hana su yancin su, wanda NLC ta jawo musu.

Malam Nasiru El-Rufa'i
Ba Gudu Ba Ja da Baya a Matakin Mu Na Korar Ma'aikata, El-Rufa'i Ya Faɗawa Buhari Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamnatin Kaduna zata ɗauki sabbin ma'aikata 10,000

A wani jawabi da mai baiwa gwamna shawara ta musamman kan yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar, El-Rufa'i yace yanzu haka gwamnatinsa ta fara aikin ɗaukar ma'aikata 10,000.

Yace wannan duk yana cikin tsarin gwamnatinsa na aiwatar da garambawul, inda zata cigaba da ɗaukar kwararrun malamai, likitoci, masu jinya da kuma ma'aikatan da suka cancanta domin gudanar da aiki mai kyau a jihar.

Wani ɓangaren jawabin yace:

"Zamu ɗauki sabbin ma'aikata 10,000 domin kudirin mu na aiwatar da garambawul ya tilasta mana ɗaukar kwararruN malamai, likitoci, masu jinya da kuma ma'aikatan da suka cancanta."

KARANTA ANAN: APC Ta Shirya Babban Gangami Yayin da Jiga-Jiganta Zasu Dira Jihar Zamfara

Ba zamu yi duk abinda ya saɓa wa kudirin mu ba

Da yake martani kan taron sulhu da aka gudanar tsakanin gwamnatinsa da NLC, gwamnan yace majlisar zartarwarsa ba zata aiwatar da duk abinda ya saɓa wa kudirinta ba, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Yace: "Gwamnatin mu ta tattauna da ministan kwadugo da samar da aikin yi, Chris Ngige, kuma ta faɗa masa ba zata iya aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma ba matuƙar ta saba wa tsarin garambawul da ta ɓullo da shi."

A wani.labarin kuma Na Gode Wa Allah da Gwamna Matawalle Ya Amsa Kira na Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC, Tsohon Kwamishina

Alamu sun gama tabbata cewa gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, zai sauya sheƙa zuwa APC.

A wani jawabin tsohon kwamishina, Alhaji Abubakar Abdullahi Tsafe, yace Matawalle ya riga ya koma APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel