Da Ɗumi-Ɗumi: Hankalin Mutane Ya Tashi Yayin da Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba da Ɗiyar Wani Ɗan Fulani

Da Ɗumi-Ɗumi: Hankalin Mutane Ya Tashi Yayin da Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba da Ɗiyar Wani Ɗan Fulani

  • Mutane sun fara ɗar-ɗar a wani yankin jihar Osun biyo bayan wani hari da yan bindiga suka kaiwa wani ɗan Fulani
  • Maharan sun kutsa har cikin gidan mutumin, inda suka yi ƙoƙarin kashe shi amma ba su samu nasara ba
  • Wasu shaidu sun tabbatar da faruwar lamarin, sun ce yan bindigan sun tafi da ɗiyar mutumin

An shiga yanayin ɗar-ɗar da tashin hankali a wani yankin jihar Osun yayin da wasu yan bindiga suka yi awon gaba da ɗiyar wani ɗan Fulani, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: COAS Ya Sake Kai Ziyara Borno, Ya Umarci Sojoji Su Ragargaji Yan Boko Haram da ISWAP

A ranar Lahadi, wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun sace ɗiyar Alhaji Bayo Fulani, a cikin gidansa dake Ga- Fulani, yankin Ora-Igbomina, karamar hukumar Ifedayo, jihar Osun.

Yan Bindiga sun sace ɗiyar wani Fulani
Da Ɗumi-Ɗumi: Hankalin Mutane Ya Tashi Yayin da Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba da Ɗiyar Wani Ɗan Fulani Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun kai hari gidan mutumin, inda suka yi ƙoƙarin hallaka shi, amma sai aka yi sa'a alburusan ba su mishi illa a jikinshi sosai ba.

Wasu shaidu da suka tabbatar da faruwar lamarin sun bayyana cewa lokacin da maharan suka gano ba su samu nasarar kashe abun harin su ba, sai suka yi awon gaba da ɗiyarsa.

Shaidun suka ce: "Maharan da suka zo da adadi mai yawa sun kutsa cikin gidan mutumin, inda suka yi ƙoƙarin kashe shi, amma basu samu nasara ba."

"Da suka fahimci haka shine suka yi awon gaba da ɗiyarsa zuwa wani wuri da ba'a san shi ba."

KARANTA ANAN: Gwarazan Sojoji Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Fatattake su a Jihar Kaduna

Duk wani ƙoƙari na tuntuɓar kakakin rundunar yan sandan Osun, DSP Opalola Yemisi, ya ci tura domin ba ta daga kiran wayar da aka mata ba kuma ba ta turo saƙo ba.

A wani labarin kuma Har Yanzun Akwai Yankunan Dake Hannun Yan Ta'adda, Shehun Borno Ga Sabon COAS

Shehun Borno, Alhaji Abubakar Elkanemi, ya yi kira gasabon hafsan soji ya maida hankali kan wasu wurare a Borno, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Sarkin yace yanzun an samu zaman lafiya a jihar idan ka kwatanta da wasu loƙuta kafin shekarar 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel