Na Gode Wa Allah da Gwamna Matawalle Ya Amsa Kira na Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC, Tsohon Kwamishina

Na Gode Wa Allah da Gwamna Matawalle Ya Amsa Kira na Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC, Tsohon Kwamishina

  • Alamu sun gama tabbata cewa gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, zai sauya sheƙa zuwa APC
  • A wani jawabin tsohon kwamishina, Alhaji Abubakar Abdullahi Tsafe, yace Matawalle ya riga ya koma APC
  • Mai taimakawa shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, ya sanar da sauya shekar gwamnan a shafinsa na facebook

Tsohon kwamishinan raya karkara a jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Abdullahi Tsafe, yace gwamna Bello Matawalle ya sauya sheƙa zuwa APC.

A jawabin da tsohon kwmishinan ya fitar, wanda aka aike wa legit.ng ranar Lahadi 27 ga watan Yuni, yace gwamna Matawalle zai tabbatar da sauya shekarsa a hukumance ranar Talata.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Hankalin Mutane Ya Tashi Yayin da Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba da Ɗiyar Wani Ɗan Fulani

Gwamna Bello Matawalle
Na Gode Wa Allah da Gwamna Matawalle Ya Amsa Kira na Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC, Tsohon Kwamishina Hoto: oyogist.com
Asali: UGC

Jam'iyya mai mulki ta yi babban kamu

Tsafe, wanda ɗaya ne daga cikin jiga-jigan APC a Zamfara, shi ne mutum na farko da ya fara kiran gwamna Matawalle ya dawo APC.

Kuma yana ɗaya daga cikin Mambobin APC dake cikin majalisar zartarwar Matawalle kafin ya rushe su baki ɗaya a farkon wannan wata.

Yace wasu yan PDP ne suka ja ra'ayin gwamnan tun lokacin da ya fara kiran shi da ya sauya sheka zuwa APC.

A jawabinsa, tsohon kwamishinan yace:

"A lokacin da nake a cikin makusantan gwamnan, na kira ye shi da ya koma APC, amma mutane da dama suka nuna rashin amincewa, amma da taimakon Allah yanzun ya amince ya dawo jam'iyya mai mulki."

"Gwamna Matawalle yayi watsi da duk kiraye-kirayen yan PDP, ya amsa kiran da na yi mishi. Mun kammala shirin tarbar gwamnan ranar Talata."

Jihar Zamfara ta yi babban nasara a siyasance

Ya ƙara da cewa da zaran Matawalle ya koma APC, to gwamnatin tarayya zata rinƙa kulawa da buƙatun jihar Zamfara yayin da zata maida hankali sosai ga jihar.

Yace: "Kasancewar jihar Zamfara maƙociyar jihar da shugaban ƙasa ya fito ne, Katsina, jihar zata fi samun cigaba idan tana cikin jam'iyya mai mulki. Barka da zuwa ranka ya daɗe."

KARANTA ANAN: Babu Wanɗanda Suka Dace da Mulkin Najeriya a 2023 Fiye da Tinubu/Ganduje, Inji TPN

Hakazalika, mai taimakawa shuagban ƙasa na yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya sanar da sauya sheƙar Matawalle.

Mr. Ahmad ya rubuta a shafinsa na Facebook:

"Zamfara ta dawo gida, barka da zuwa gwamna Matawalle."

A wani labarin kuma Danbarwa Ta Ɓarke a Jam'iyyar APC Bayan Sanar da Ɗan Takarar Gwamna a Zaɓen Dake Tafe

Danbarwa ta ɓarke a jam'iyyar APC reshen jihar Anambra biyo bayan bayyana wanda ya lashe zaɓen fitar da ɗan takara.

Ministan ƙwadugo, Chris Ngige, yace kwata-kwata ba'a gudanar da wani zaɓe ba a jihar, ya kuma bada shawarar 29 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel