Babu Wanɗanda Suka Dace da Mulkin Najeriya a 2023 Fiye da Tinubu/Ganduje, Inji TPN

Babu Wanɗanda Suka Dace da Mulkin Najeriya a 2023 Fiye da Tinubu/Ganduje, Inji TPN

  • Shugaban ƙungiyar magoya bayan Tinubu (TPN) reshen jihar Kano, Muhammad Tajo, yace babu kamar Tinubu a 2023
  • Tajo ya yi kira ga gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da ya amince ya nemi mataimakin shugaban ƙasa
  • Yace Tinubu da Ganduje sun dace kuma sun cancanta su jagoranci yan Najeriya a zaɓen 2023

Jagoran siyasa a jihar Kano kuma shugaban ƙungiyar magoya bayan Tinubu a jihar (TPN), Muhammad Tajo Nagoda, ya bayyana cewa babu wanda ya dace ya ɗare mulkin shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2023 sama da jigon APC, Bola Tinubu.

KARANTA ANAN: Har Yanzun Akwai Yankunan Dake Hannun Yan Ta'adda, Shehun Borno Ga Sabon COAS

Ya faɗi haka ne a ƙarshen mako yayin da yake fura da jaridar Vanguard, ya kuma yi kira ga gwamna Ganduje na jihar Kano ya amince ya nemi mataimakin shugaban ƙasa.

Tajo ya bayyana Bola Tinubu a matsayin mutumin da yan Najeriya suke buƙata a halin da ake ciki.

Bola Tinubu Da Gwamna Ganduje
Babu Wanda Ya Dace da Mulkin Najeriya a 2023 Fiye da Tinubu, Inji TPN Hoto: thecolumnist.com.ng
Asali: UGC

Yace: "Gare mu yan ƙungiyar TPN a Kano, mun yi imanin cewa akwai buƙatar ingantaccen shugaba a 2023, shugaban dake da ƙwarin guiwar fuskantar duk wani ƙalubalen siyasa dbya tinkare shi."

"A wurin mu wannan shi yafi dacewa da Najeriya a zaɓen 2021 kuma ba kowa bane illa Alhaji Bola Ahmed Tinubu. Mu anan arewa bamu da wanda ya fishi dacewa."

KARANTA ANAN: Danbarwa Ta Ɓarke a Jam'iyyar APC Bayan Sanar da Ɗan Takarar Gwamna a Zaɓen Dake Tafe

Tajo Ya roƙi Ganduje ya amince ya nemi nataimakin Tinubu

Da yake kare maganarsa ta Ganduje ya nemi mataimakin shugaban ƙasa, Tajo ya yi watsi da banbancin ƙabila da addini da wasu yan Najeriya ke maida hankali a akai.

Yace: "Duk masu tsayawa duba ƙabila da adini fiye da kwarewa da cancanta wanda muka gani a Tinubu da Ganduje, to ba su son gaskiya wajen zaɓen shugabanni nagari."

A wani labarin kuma Jiga-Jigan Siyasa a Gombe Sun Yi Watsi da Matakin Sanata Ɗanjuma Goje a 2023

Matakin da sanata Ɗanjuma Goje ya ɗauka na jingine siyasa a shekarar 2023 ya samu naƙasu daga masoyansa, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Goje, wanda tsohon gwamnan jihar Gombe ne, kuma sanata a zango na uku, an nemi ya cigaba da rike muƙaminsa na sanata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262