PDP Ta Hasala, Ta Garzaya Kotu Domin Dakatar da Matawalle Daga Komawa APC

PDP Ta Hasala, Ta Garzaya Kotu Domin Dakatar da Matawalle Daga Komawa APC

  • Jam'iyyar PDP ta tunzura bayan da gwamnan Zamfara ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
  • Bayan tabbatar da sauya shekar ta gwamna Matawalle, an ce jam'iyyar PDP ta garzaya kotu
  • An sanar da cewa, Gwamnan Yobe ya ce za a tarbi gwamnan na Zamfara a cikin jihar ta sa

Majiyoyi da yawa sun tabbatar da cewa, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a gobe zai koma jam'iyyar APC daga jam'iyyar PDP, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan yasa PDP ta ce za ta dauki matakin doka domin dakatar da gwamnan na Zamfara daga barin jam'iyyarsu.

Ba tare da bata lokaci ba, an tattaro cewa za a ambaci karar da wasu jiga-jigan PDP suka shigar kan sauya shekar Matawalle a yau a kotu.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Harbe Mata Mai Juna Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Mijinta

PDP Ta Hasala, Ta Garzawa Kotu Saboda Gwamna Matawalle Ya Koma APC
Tutar jam'iyyar PDP | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jam'iyyar APC ta tabbatar da sauya shekar gwamna Matawalle daga jam'iyyar PDP

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni ya tabbatar da sauya shekar na Matawalle a wata wasikar gayyata da ya gabatar ranar Asabar.

Buni, a cikin wasikar da shi da kan sa ya sanya hannu a kai, ya ce za a tarbi gwamnan na Zamfara a gidan Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau gobe.

A cewar gwamnan na Yobe, Matawalle zai koma APC tare da magoya bayansa da dama.

Hakazalika, a wani gidan rediyo na cikin jihar Zamfara, an yi sanarwar cewa gwamnan zai sauya sheka zuwa APC gobe. Sanarwar da aka watsa ta jiya ta fito ne daga bakin Alhaji Ibrahim Dosara.

Yawan sauya-sheka da ake yi zuwa APC ya sa an huro wuta a tunbuke Shugaban PDP

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wasu matasa a jam’iyyar PDP sun fara kiran ayi maza-maza a sauke shugaban jam’iyya na kasa, Prince Uche Secondus.

Matasan jam’iyyar na yankin Kudu a karkashin tafiyar South-South Youth Vanguard, suka fitar da jawabi, su na Allah-wadai da asarar da jam’iyyar ta ke ta yi.

Shugaban South-South Youth Vanguard, James Efe Akpofure, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar hamayyar su kawo karshen ficewa daga PDP da manya su ke yi.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Fasinjoji Sun Makale a Daji Bayan da Jirgin Kasa Ya Lalace a Kaduna

Bayan Gwamna Matawalle, Jigo a Jam'iyyar APGA Ya Bi Sahu Zuwa Jam'iyyar APC

A wani labarin, Tsohon sakataren jam'iyyar APGA, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, ya sauya sheka daga jam'iyyar ya koma tare da gwamnan jihar Zamfara, Bello Mattawalle zuwa jam'iyyar APC mai mulki, Daily Trust ta ruwaito.

Shinkafi tsohon dan takarar Gwamna na APGA kuma sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar a cikin wata wasika zuwa ga Sakataren Jam’iyyar na kasa ya sanar da murabus dinsa a matsayin memba na jam’iyyar kuma Sakataren kwamitin amintattu.

A cewar wasikar ta Shinkafi:

“Wannan shi ne a hukumance na mika takardar murabus a matsayin memba na jam'iyyar APGA kuma Sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar wanda zai fara daga ranar da wasikar ta kasance.
"Na yanke shawarar yin murabus ne bayan tuntuba da nayi da magoya baya na, da dangi na, da abokaina na siyasa a jihar ta Zamfara da sauran 'yan Najeriya wadanda suka samar da wani bangare na goyon baya na."

Asali: Legit.ng

Online view pixel