Bayan Gwamna Matawalle, Jigo a Jam'iyyar APGA Ya Bi Sahu Zuwa Jam'iyyar APC

Bayan Gwamna Matawalle, Jigo a Jam'iyyar APGA Ya Bi Sahu Zuwa Jam'iyyar APC

  • Jim kadan bayan ficewar gwamnan jihar Zamfara zuwa jam'iyyar APC, tsohon sakataren APGA shima ya bi sahu
  • Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya fice daga jam'iyyar APGA zuwa APC kamar yadda ya bayyana a wata wasika
  • Gwamnan an bayyana komawarsa jam'iyyar APC ne a yau Lahadi ta shafin wani jigon APC na Facebook

Tsohon sakataren jam'iyyar APGA, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, ya sauya sheka daga jam'iyyar ya koma tare da gwamnan jihar Zamfara, Bello Mattawalle zuwa jam'iyyar APC mai mulki, Daily Trust ta ruwaito.

Shinkafi tsohon dan takarar Gwamna na APGA kuma sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar a cikin wata wasika zuwa ga Sakataren Jam’iyyar na kasa ya sanar da murabus dinsa a matsayin memba na jam’iyyar kuma Sakataren kwamitin amintattu.

KU KARANTA: 'Yan yankin Neja Delta sun ba Buhari wa'adin kwanaki 90 ya sake fasalin Najeriya

Gwamna Matawalle da Jigo a Jam'iyyar AFGA Sun Sauya Sheka Zuwa APC
Dr Sani Abdullahi Shinkafi | Hoto: herald.ng
Asali: UGC

A cewar wasikar ta Shinkafi:

“Wannan shi ne a hukumance na mika takardar murabus a matsayin memba na jam'iyyar APGA kuma Sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar wanda zai fara daga ranar da wasikar ta kasance.
"Na yanke shawarar yin murabus ne bayan tuntuba da nayi da magoya baya na, da dangi na, da abokaina na siyasa a jihar ta Zamfara da sauran 'yan Najeriya wadanda suka samar da wani bangare na goyon baya na."

Ya nuna godiya ga Gwamnan Jihar Anambra wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar APGA na kasa da kuma Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar, Cif Willie Obiano da sauran jiga-jigan jam'iyyar.

Ya kara da cewa:

"Ina yi wa jam'iyyar fatan alheri da kuma Farfesa Chukwuma Soludo, dan takarar jam'iyyarmu a zaben gwamnan Anambra mai zuwa ranar 6 ga Nuwamba 2021, ina yi masa fatan samun nasara a zaben."#

Gwamnan Zamfara, Matawalle, Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da sauya sheƙar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, daga jam'iyyar PDP zuwa Jam'iyya mai mulki ta APC.

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da mai taikawa shugaban ƙasa Buhari ta ɓangaren yaɗa labarai, Bashir Ahmad, yayi a shafinsa na dandalin sada zumunta wato Facebook.

Bashir Ahmad, ya rubuta a shafinsa cewa:

"Zamfara ta dawo gida, lale marhabun gwamna Matawalle."

KU KARANTA: Cikakken Bayani: Fusatattun 'yan PDP sun yi garkuwa da jami’an zabe a Jigawa

Siyasar Kano: Jerin Wadanda Ake Kyautata Zaton Za Su Gaji Kujerar Ganduje a 2023

A wani labarin, Gabanin zaben gwamna a 2023 a jihar Kano, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce wakila da jam'iyya ne za su tsayar da wanda zai fito a matsayin wanda zai gaje shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan na Kano ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da ‘yan jarida a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni.

Legit.ng ta tattaro cewa Gwamna Ganduje ya yi wannan bayanin ne bayan tsoffin ‘yan takarar gwamna uku a zabukan da suka gabata a karkashin jam’iyyun siyasa daban-daban sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.