Yanzu-Yanzu: Fasinjoji Sun Makale a Daji Bayan da Jirgin Kasa Ya Lalace a Kaduna

Yanzu-Yanzu: Fasinjoji Sun Makale a Daji Bayan da Jirgin Kasa Ya Lalace a Kaduna

  • Jirgin kasa ya lalace a hanyar Kaduna zuwa Abuja, lamarin da ya jefa fasinjoji cikin damuwa
  • An ruwaito cewa, jirgin ya tsaya a hanya har sau biyu kafin daga bisani ya tsaya gaba daya
  • An ce, an tuntubi cibiyar gyara, kuma ana sa ran za a gyara jirgin nan da awanni biyu masu zuwa

Daruruwan fasinjoji da ke cikin jirgin kasa na Abuja/Kaduna a yanzu haka sun makale a Dutse, yankin Kaduna, yayin da jirgin yasamu nakasu 'yan mintoci da fara tafiya.

Daily Trust ta ruwaito cewa minti biyar bayan jirgin ya tashi daga Tashar Rigasa da ke Kaduna, sai ya samu matsalar inji.

Sau biyu, jirgin ya tsaya kafin ya isa Dutse, inda daga karshe ya lalace.

Midat Joseph, mataimakin Sakatare na kasa na kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), wanda na daya daga cikin fasinjojin, ya ce jirgin ya samu matsala ne da misalin karfe 7 na safe.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta magantu kan yunkurin hana shigo da tukunyar gas Najeriya

Yanzu-Yanzu: Fasinjoji Sun Makale a Daji Bayan da Jirgin Kasa Ya Lalace a Kaduna
Yayin da fasinjoji ke jiran a gyara jirgin | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa:

“Na bar gidana tun da karfe 5 na safe don shiga jirgin karfe 6:40 na safe amma abin takaici ga ni a cikin kurmin nan. Wannan ba shine karo na farko da zan fara fuskantar wannan matsalar ba."

Wani fasinja, ya ce shi ma ya samu irin wannan matsalar a ranar Asabar, yana mai cewa sun kwashe sa’o’i shida kafin su je Abuja.

A kalamansa:

“Wannan abin takaici ne. A ranar Asabar, mun kwashe awanni biyar daga Abuja zuwa Kaduna. Mun bar Abuja karfe 6: pm amma ba mu iso Kaduna ba sai 11: pm.”

Wani Injiniyan NRC, wanda ya yi wa fasinjojin jawabi, ya gaya musu cewa zai dauke su awanni biyu kafin su gyara jirgin.

Ya ce:

“Muna matukar ba ku hakuri, abun motsa jirgin ya lalace. Mun tuntubi tashar jirgin kasa ta Idu don wani abun motsa jirgin. Zai dauke su awanni biyu kafin su iso nan."

Jirgin Kasa Da Ya Taso Daga Legas Zuwa Zariya Ya Yi Hatsari a Jihar Kaduna

Wani jirgin kasa mai dauke da bututun ruwa daga jihar Legas zuwa Zariya a jihar Kaduna ya yi hatsari a wani yankin jihar ta Kaduna.

Hatsarin wanda ya afku a yankin Unguwar Kanawa da ke Kaduna ya tilasta wa jirgin tashi daga layin dogo, wanda hakan ya sa biyar daga cikin taragon jirgin kaucewa daga kan hanyar.

Duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba a lamarin, injiniyan da ke kula da ayyukan Arewa na kamfanin jirgin kasa na Najeriya, Haruna Ahmed ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa hatsarin jirgin ya faru ne sakamakon lalata hanyoyin jirgin da wasu bata-gari suka yi.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Harbe Mata Mai Juna Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Mijinta

'Yan Bindiga Sun Harbe Mata Mai Juna Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Mijinta

An dauki tsawon sa’o’i 3 a jeji, jirgin kasan Najeriya ya tsaya a hanya

Wani labarin, a ranar Lahadi, 3 ga watan Junairu, 2020, jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya sake lalacewa, Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.

Rahoton ya bayyana cewa jirgin kasan ya lalace a hanya ne bayan dawowa daga garin Kaduna.

Bayan an dauko fasinjoji daga Rigasa, jihar Kaduna, an shirya za a tafi Idu, garin Abuja, sai wannan jirgi ya mutu a daidai kauyen da ake kira Akere.

Jaridar ta ce a wannan kauye ne kanikawan hukumar jirgin kasan Najeriya na NRC su ka shafe tsawon sa’o’i uku su na ta kokarin gyara jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel