Gwamnatin Buhari ta magantu kan yunkurin hana shigo da tukunyar gas Najeriya
- Gwamnatin Buhari ta bayyana cewa, ba ta shirin dakatar da shigo da tukwanen gas Najeriya
- A cewarsa wani jigo a gwamnati, kasar ba ta isassun tukwanen iskar idan aka kwatanta da wasu kasashe
- A cewarsa, Najeriya na bukatar ci gaba da shigo da tukwanen saboda cimma manufar rage yawaitar hayaki
Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da wani shiri na nan take don hana shigowa da tunkwanen gas a wani bangare na fadadawa da aiwatar da harkar a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
Dayo Adesina, babban mataimaki na musamman kan harkar iskar gas a ofishin Mataimakin Shugaban kasa, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.
Ya ce gwamnati na aiki kan fara gina na ta na cikin gida kafin ta yi tunanin hana shigowa da gas din kwata-kwata.
KU KARANTA: Wata Sabuwa: Sojoji sun afkawa ofishin 'yan sanda domin kubutar da masu laifi
A cewar Adesina, wanda kuma shi ne Manajan Shirye-shirye na fadadawa da aiwatar da LPG na kasa, har yanzu Najeriya na da gibin tukwane da yawa da za ta cike yayin ganawa a shirin fadada LPG.
Ya bayyana cewa shirin shine a samar da LPG zuwa kauyukan da ke nesa da kuma hana amfani da itacen girki da sauran man da ke da illa ga muhalli.
Minista ya bayyana adadin tukwanen gas da ake dasu a Najeriya da sauran kasashe
Adesina ya ce daga cikin yawan al’ummar kasar sama da miliyan 200, akwai kusan tukwane miliyan biyu na gas, wanda ya ce, hakan bai wadatar ba idan aka kwatanta da sauran kasashe.
Ya yi nuni da cewa, kasar Brazil, mai yawan al'umma irinta Najeriya, tana da yawan tukwane miliyan 150 da karin samar da miliyan biyar a shekara, in ji NNN.
Ya ce ga Indiya, yawan tukwanen gas ya haura miliyan 100 yayin da Mexico ke da yawan tukwane kusan miliyan 100.
Legit.ng Hausa ta lura cewa, duba da wannan kididdiga, Adesina ya bayyana cewa:
“Hana shigo da kaya daga kasashen waje ba zai magance matsalar ba. Zai kara dagula matsalar ne. ”
Ya ce akwai bukatar gwamnati ta hanzarta shigo da tukwanen gas a duk fadin kasar idan har za ta ci gaba da kiyaye manufarta da ta dauka na rage fitar da hayaki.
KU KARANTA: Kungiyar ESN Ta Kashe Bokanta Bisa Yin Tsafin da Bai Yi Tasiri Kan ’Yan Sanda Ba
Shinkafa Ta Wadata a Najeriya, Saura a Fara Fitarwa Kasashen Waje, in Ji RIFAN
A wani labarin, Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN), ta ce noman shinkafa a kasar ya karu daga tan miliyan biyu a 2015 zuwa tan miliyan tara a 2021, Daily Nigerian ta ruwaito.
Da yake bayyana hakan a Kaduna a ranar Alhamis, Shugaban RIFAN, Aminu Goronyo, ya ce duba da yawan kayan da ake sarrafawa a yanzu, Najeriya ta shirya zama kasar da zata ke fitar da shinkafa zuwa kasashen waje.
A cewarsa:
“Kafin zuwan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, mun saba samar da kimanin shinkafa tan miliyan biyu a shekara.
“A yau, za mu iya alfahari da tan miliyan tara a shekara; akwai bambanci sosai kuma yanzu za mu iya cewa balo-balo Najeriya ta wadatu da shinkafa.''
Asali: Legit.ng