Zarah Ado Bayero: Abin da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano da Yusuf Buhari zai aura

Zarah Ado Bayero: Abin da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano da Yusuf Buhari zai aura

An fara shirye shiryen auren dan gidan Shugaban kasa Muhummadu Buhari, Yusuf Buhari gadan gadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ranar Lahadi, wakilcin shugaban kasa suka ziyarci fadar Sarkin Kano inda aka tattauna batun auren.

Yusuf Buhari da Zarah Ado Bayero
Yusuf Buhari da Zarah Ado Bayero. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Badaru, shine ya jagoranci tawagar shugaban kasa zuwa fadar shugaban kasa tare da wasu manyan kusoshin gwamnati.

DUBA WANNAN: 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

Daily Trust ta ruwaito cewa Yusuf, da daya tilo ga Shugaba Buhari ya gamu da wacce ta sace zuciyar tasa, Zarah Ado Bayero, a kasar Ingila inda duka su biyu suka yi karatu.

Wadannan wasu muhimman abubuwa ne da ya kamata ku sani game da sabuwar sirikar shugaban kasar:

Yar Sarkin Bichi

Zarah Ado Bayero yar 19 ya ce ga sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, wanda shine da na hudu a jerin yayan marigayi Alhaji Ado Bayero, tsohom sarkin Kano. Babanta, bayan kasancewar sa sarki, shine shugaban kamfanin sadarwa na 9mobile. Shine da na farko da aka haifa a gidan sarautar Kano na yanzu da aka fi sani da Gidan Dabo.

Shine Hakimin Fagge,Tarauni da Nassarawa da ke birnin Kano kafin nada a shi a matsayin sarkin yanka da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi.

KU KARANTA: An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

Alakar ta da Sokoto

Mahaifiyar Zarah, Farida Imam, ya ce ga fittaccen malami a Kano, Mal Abubakar Imam (Imamu Galadanci), tsohon shugaban bankin Afribank Plc, Sultan na Sokoto, Muhammad Saad Abubakar |||, yana auren yar uwar Farida.

Karatu

Zarah ita ce ta biyu a jerin yayan sarkin kuma ta karanta harkar zanen gida (Architecture) a kasar Birtaniya.

A wani labarin, kun ji wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel