Da Ɗuminsa: Ɗan majalisar jihar Nigeria ya yanke jiki ya faɗi matacce

Da Ɗuminsa: Ɗan majalisar jihar Nigeria ya yanke jiki ya faɗi matacce

  • Allah ya yi wa dan majalisar dokokin jihar Delta Honarabul Kenneth Ogba rasuwa a ranar Lahadi
  • Honarabul Kenneth Ogba ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya fadi bayan hallartar wani taro a garin Isoko
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa mai dakinsa Mrs Elizabeth Ogba itama an kwantar da ita asibiti saboda razana da ta yi

Ɗan majalisar jihar dokoki na jihar Delta, Honarabul Kenneth Ogba ya riga mu gidan gaskiya, Vanguard ta ruwaito.

Ogba, wanda ke wakiltar mazabar Isoko South ta 1 a majalisar dokoki na jihar ya rasu ne a yammacin ranar Lahadi 27 ga watan Yuni a cewar rahotanni.

Da Ɗuminsa: Ɗan majalisar jihar Nigeria ya yanke jiki ya faɗi matacce
Da Ɗuminsa: Ɗan majalisar jihar Nigeria ya yanke jiki ya faɗi matacce
Asali: Original

DUBA WANNAN: Zarah Ado Bayero: Abin da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano da Yusuf Buhari zai aura

LIB ta ruwaito cewa an gano cewa ɗan majalisar ya yanke jiki ya faɗi ne bayan hallartar wani taro a ƙaramar hukumar Isoko South a jihar

An garzaya da shi wani asibiti a garin inda likitoci da ke aiki suka sanar da cewa ya rasu.

Wata majiya da ta nemi a sakayya sunanta ta ce an ajiye gawarsa a ɗakin ajiye gawarwaki na asibitin Oleh, matarsa Mrs Elizabeth Ogba itama an kwantar da ita asibiti saboda razana da ta yi.

Kawo yanzu ba a sanar da anihin abin da ya yi sanadin rasuwar dan majalisar ba.

KU KARANTA: Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

Rasuwarsa na zuwa ne fiye da watanni biyar bayan rasuwar tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Delta da ya rasu a Asaba.

An zaɓi Ogba ne a watan Maris domin ya maye gurbin Owhefere a matsayin shugaban masu rinjaye.

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164