Danbarwa Ta Ɓarke a Jam'iyyar APC Bayan Sanar da Ɗan Takarar Gwamna a Zaɓen Dake Tafe

Danbarwa Ta Ɓarke a Jam'iyyar APC Bayan Sanar da Ɗan Takarar Gwamna a Zaɓen Dake Tafe

  • Danbarwa ta ɓarke a jam'iyyar APC reshen jihar Anambra biyo bayan bayyana wanda ya lashe zaɓen fitar da ɗan takara
  • Ministan ƙwadugo, Chris Ngige, yace kwata-kwata ba'a gudanar da wani zaɓe ba a jihar, ya kuma bada shawarar 29 ga watan Yuni
  • Kakakin APC reshen jihar, Okelo Madukaife, ya nesanta jam'iyyarsa da sakamakon da ake yaɗawa

Rikici ya ɓarke a jam'iyyar APC biyo bayan bayyana, Sanata Andy Uba, a matsayin ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen gwamnan Anambra dake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Jiga-Jigan Siyasa a Gombe Sun Yi Watsi da Matakin Sanata Ɗanjuma Goje a 2023

Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani kuma gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, shine ya bayyana sakamakom zaɓen a Otal ɗin Tulip, Awka da safiyar Lahadi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamna Abiodun yace Uba shine ya lashe zaɓen fidda gwani da ƙuri'u 230,201 yayin da ya lallasa na kusa da shi, Johnbosco Onunkwo, wanda ya samu ƙuri'u 28,746.

Sanata Andy Uba
Danbarwa Ta Ɓarke a Jam'iyyar APC Bayan Sanar da Ɗan Takarar Gwamna a Zaɓen Dake Tafe Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ngige yace Ba'a gudanar da zaɓen fidda ɗan takara ba

Ministan ƙwadugo da samar da aikin yi, Chris Ngige, ya bayyana cewa sam ba'a gudanar da zaɓen fitar da ɗan takara ba.

Ministan ya baiwa jam'iyyar APC shawarar ta shirya zaɓen fitar da ɗan takara a ranar 29 ga watan Yuni.

Hakazalika, 11 daga cikin mutum 14 dake neman jam'iyyar APC ta tsayar da su takara sun bayyana cewa ba'a gudanar da zaɓen ba.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Gwamnan Zamfara, Matawalle, Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

APC a Anambra ta yi watsi da sakamakon zaɓen da ake yaɗawa

A wani jawabi da kakakin jam'iyyar APC reshen jihar Anambra, Okelo Madukaife, ya fitar, ya nesanta jam'iyyarsu da rahoton zaɓen da ake yaɗawa.

Yace: "An jawo hankalin mu kan wani rahoto dake yawo a kafafen watsa labarai ba tare da sanya hannun kowa ba, kuma ana danganta shi da sakamakom zaɓen fidda ɗan takara na jam'iyyar APC a Anambra."

"Sakamakon ba shi da alaƙa da zaɓen fidda ɗan takarar APC a zaɓen gwamnan Anambra, wanda kwata-kwata ba'a gudanar da shi ba."

"Muna jiran kwamitin riƙo na APC ta ƙasa ya saka ranar zaɓen cikin jadawalin da hukumar zaɓe ta fitar."

A wni labarin kuma PDP Ta Dare Gida Biyu, Ta Tsayar da Yan Takara 2 a Zaɓen Dake Tafe

Rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP ya ƙara tsananta yayin da aka gudanar da zaɓen fidda ɗan takara biyu a jihar Anambra.

Jam'iyyar ta dare gida biyu inda kowane ɓangare ya gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar gwamnan Anambra a wuri daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: