Jiga-Jigan Siyasa a Gombe Sun Yi Watsi da Matakin Sanata Ɗanjuma Goje a 2023

Jiga-Jigan Siyasa a Gombe Sun Yi Watsi da Matakin Sanata Ɗanjuma Goje a 2023

  • Matakin da sanata Ɗanjuma Goje ya ɗauka na jingine siyasa a shekarar 2023 ya samu naƙasu daga masoyansa
  • Goje, wanda tsohon gwamnan jihar Gombe ne, kuma sanata a zango na uku, an nemi ya cigaba da rike muƙaminsa na sanata
  • Masoyan sanatan sun yi barazanar garzayawa kotu idan yaƙi amincewa da kiran da ake masa

Jiga-jigan siyasa a jihar Gombe da masu faɗa a ji sun yi watsi da matakin sanata Ɗanjuma Goje (APC, Gombe ta tsakiya) na jingine harkar siyasa a shekarar 2023, kamar yadda the cable ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Gwamnan Zamfara, Matawalle, Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

Goje, wanda yake wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattijai a karo na uku, ya ɗauki matakin aje siyasa ne domin ya baiwa matasa dama su ɗora daga inda ya tsaya.

Amma manyan masu faɗa a ji na jihar, yayin wani taron bayyana ɗumbin ayyukan da Ɗanjuma Goje yayi wa al'ummar jihar Gombe a filin wasan Kumoh Township, ƙaramar hukumar Akko ranar Asabar, sun yi kira ga Sanata Goje, ya sake nazari a kan matakinsa.

Hakazalika, sun yi barazanar cewa matuƙar bai karɓi kiran da suke mishi ba to zasu garzaya gaban kotu.

Sanata Ɗanjuma Goje da Pantami
Jiga-Jigan Siyasa a Gombe Sun Yi Watsi da Matakin Sanata Ɗanjuma Goje a 2023 Hoto: Hausa Daily times FB Fage
Asali: Facebook

Babban Jigon siyasa a Arewa Maso Gabas

Da yake jawabi a wurin taron, tsohon mataimakin gwamna, Sanata Joshua Lidani, yace siyasar Sanata Goje ta amfanar da jihar Gombe dama yankin arewa maso gabas baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa Goje ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa hukumar raya yankin arewa maso gabas.

Sanata Lidani ya roƙi Goje da ya taimaka ya amsa kiran mutanen da yake wakilta na canza shawarar jingine siyasa.

Hakanan, da yake jawabi, shugaban ƙaramar hukumar Akko, Abubakar Barambu, yace:

"Mutanen mu sun umarci ne in sanar da cewa sun amince da gwamna Yahaya ya cigaba da jagorantar al'amuran jihar Gombe."

"Hakanan, sun nemi in sanar da cewa sun amince da Sanata Ɗanjuma Goje ya cigaba da wakiltar su a Gombe ta tsakiya har gaban 2023. Idan shi ya gaji, to al'umma ba su gaji da wakilcin shi ba."

"Idan suka ƙi amincewa da kiram mu, to a shirye muke mu garzaya gaban kotu, dan Allah ku saurare mu, ku sake tsayawa takara."

KARANTA ANAN: PDP Ta Dare Gida Biyu, Ta Tsayar da Yan Takara 2 a Zaɓen Dake Tafe

Jigon siyasar da jihar Gombe ke taƙama da shi

A jawabinta, yar majalisar wakilan tarayya, Aishatu Jibril Dukku (APC, Mai wakiltar Dukku/Nafaɗa), ta bayyana cewa sanata Goje ya bada gudummuwa wajen cigaban jihar Gombe, yankin arewa maso gabas da ƙasa baki ɗaya.

Dukku, wacce tsohuwar ministar Ilimi ce, ta roƙi Sanata Goje da yayi hakuri kada ya aje siyasa a shekarar 2023 dake tafe.

Tace: "Mun zo nan ne domin mu tilasta mishi kada ya jingine harkar siyasa. Ina magana ne a madadin tawagar iyalan siyasarsa, kada ya tabbatar da maganar aje siyasar da yayi."

Dailytrust ta ruwaito cewa sunan sanata Ɗanjuma Goje, na daga cikin sunayen da ake tsammanin zasu iya ɗarewa kujerar shugabancin jam'iyyar APC ta ƙasa.

A wani labarin kuma An Kuma, Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Wani Basarake, Sun Saki Matarsa

Wasu mutane ɗauke da makamai da ake zargin masu garkuwa ne sun yi awon gaba da wani basarake a jihar Ekiti.

Oba Benjamin Oso na Eda Ile, ya fita gonarsa shi da matarsa yayin da yan bindigan suka kai masa hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel