Har Yanzun Akwai Yankunan Dake Hannun Yan Ta'adda, Shehun Borno Ga Sabon COAS

Har Yanzun Akwai Yankunan Dake Hannun Yan Ta'adda, Shehun Borno Ga Sabon COAS

  • Shehun Borno, Alhaji Abubakar Elkanemi, ya yi kira ga sabon hafsan soji ya maida hankali kan wasu wurare a Borno
  • Sarkin yace yanzun an samu zaman lafiya a jihar idan ka kwatanta da wasu loƙuta kafin shekarar 2015
  • Ya kuma roƙi sabon COAS ɗin da ya taimaka ya maida manoma yankunan su sabida mutanen Borno Manoma ne

Mai martaba shehun Borno, Alhaji Abubakar Elkanemi, ya roƙi sabon hafsan sojin ƙasa, Manjo janar Farouk Yahaya, da ya ƙara maida hankali kan wasu wurare da har yanzun ba'a iya zuwa saboda ayyukan yan ta'addan Boko Haram, kamar yadda premiun times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Danbarwa Ta Ɓarke a Jam'iyyar APC Bayan Sanar da Ɗan Takarar Gwamna a Zaɓen Dake Tafe

Basaraken yayi wannan kira ne ranar Jumu'a da yamma yayin da ya karɓi baƙuncin sabon COAS a fadarsa dake Maiduguri.

Sarkin yace duk da cigaban da aka samu a yaƙin da ake da masu tada ƙayar baya daga 2015 zuwa yau, amma har yanzin akwai wuraren da ba'a iya zuwa saboda yawaitar hare-haren yan ta'adda.

Sabon hafsan sojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya
Har Yanzun Akwai Yankunan Dake Hannun Yan Ta'adda, Shehun Borno Ga Sabon COAS Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yace a halin yanzun babu wata ƙaramar hukuma dake hannun yan ta'addan, ba kamar baya ba kafin 2015, lokacin da ƙananan hukumomi 17 ke ƙarkashin ikon su.

Yace: "Mun sha wahala sosai a hannun yan ta'adda idan ka kwatanta da zaman lafiyan da muka samu yanzun."

"Akwai wani lokaci da bamu da sabis ɗin waya, filayen jirgin mu basa aiki, ba tsaro a dukkan hanyoyin mu in banda hanyar Maiduguri zuwa Kano, kuma an kashe mutanen mu da dama harda masu riƙe da sarautar gargajiya."

"Kafin 2015, kimanin ƙananan hukumomi 17 ne ke hannun yan ta'addan Boko Haram, amma yanzun duk sun dawo karƙashin kulawar jami'an soji."

KARANTA ANAN: Jiga-Jigan Siyasa a Gombe Sun Yi Watsi da Matakin Sanata Ɗanjuma Goje a 2023

Shehun Borno ya roƙi COAS ya taimaka manoma su koma sana'arsu

Alhaji Elkanemi ya bayyana cewa mutane na jin tsoron komawa wasu daga cikin ƙauyukan su.

Yace: "Muna roƙon shugaban rundunar sojin ƙasa yayi amfani da duk wata dama da yake da ita, ya taimaka wa manoma su koma gonakinsu, saboda mafi yawan mutanen Borno manoma ne."

"Wurare kamar Baga, Krenoa, Marte, Gamboru-Ngala, waɗanda suke da iyaka da tafkin Chadi, sune inda mafi yawan mutanen wurin manoma ne da masu kamun kifi."

A wani labarin kuma Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya ƙara jaddada maganarsa kan cewa duk wanda ya ɗauki makami ya yaƙi Najeriya zai fuskanci hukunci.

Shugaban yace matasa na da rawar da zasu taka domin gina goben su da kuma ƙasar su, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262