Cikakken Bayani: Fusatattun 'yan PDP sun yi garkuwa da jami’an zabe a Jigawa

Cikakken Bayani: Fusatattun 'yan PDP sun yi garkuwa da jami’an zabe a Jigawa

  • Ma'aikatan zabe sun hadu da fushin matasan jam'iyyar PDP a jihar Jigawa bayan zaben kananan hukumomi
  • Jami'in tattara sakamakon zabe ya arce bayan kammala zaben, wannan yasa aka tsare dukkan jami'an zaben
  • A halin yanzu jami'an na tsare cikin wata makarantar firamare inda suka kwana tun jiya Asabar

Rahotanni da Legit.ng Hausa ke samu sun bayyana cewa, mambobin jam’iyyar PDP da ke fusace a yanzu haka suna rike da jami’an aikin zabe saboda rashin bayyana sakamakon zaben da ake ganin dan takarar jam’iyyar ya lashe a wani sashi a karamar hukumar Birnin Kudu.

Hukumar zaben jihar ta gudanar da zabukan kananan hukumomi a fadin kananan hukumomi 27 na jihar a ranar Asabar, Premium Times ta ruwaito.

An tsare jami'an ne a rumfar zaben tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a yankin Chiyako da ke karamar hukumar Birnin Kudu.

Jami'in tattara sakamakon zabe a rumfar an rawaito cewa ya tsere ba tare da bayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben ba duk da cewa an kirga kuri'un.

KU KARANTA: 'Yan yankin Neja Delta sun ba Buhari wa'adin kwanaki 90 ya sake fasalin Najeriya

Yanzu-Yanzu: Fusatattun 'yan PDP sun yi garkuwa da jami’an zabe dake kan aiki a Jigawa
Hotunan inda aka tsare jami'an zabe a Jigawa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Babandi Ibrahim, ya shaidawa manema labarai a ranar Lahadi cewa bacewar jami’in tattara sakamakon zaben ne ya sa masu zaben suka fusata suka yi garkuwa da jami’an zaben.

Jami’an sun kwana a cikin wani aji a wata makarantar firamare inda aka tsare da su tun da yammacin ranar Asabar.

Mista Ibrahim ya dage cewa dole ne jami'in tattara sakamakon zaben ya koma rumfar zaben ya bayyana sakamakon zaben kamar yadda dokar zabe ta tanada.

Masu zanga-zangar sun kulle dukkanin jami’an zaben ciki har da Ramlah Isah, diyar tsohon shugaban jam’iyyar APC a Birnin Kudu, Yusuf Isah.

Mista Isah a yanzu haka shi ne mataimakin shugaban karamar hukumar Birnin Kudu mai barin gado.

Masu zanga-zangar sun yi alwashin cewa ba za su sake mutanen ba har sai lokacin da aka gabatar da sakamakon zaben, wanda aka yi imanin cewa PDP ce ta lashe.

Kalli hotunan yadda aka tsare su:

Yanzu-Yanzu: Fusatattun 'yan PDP sun yi garkuwa da jami’an zabe dake kan aiki a Jigawa
Hotunan inda aka tsare jami'an zabe a Jigawa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yanzu-Yanzu: Fusatattun 'yan PDP sun yi garkuwa da jami’an zabe dake kan aiki a Jigawa
Hotunan inda aka tsare jami'an zabe a Jigawa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Zamfara, Matawalle, Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da sauya sheƙar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, daga jam'iyyar PDP zuwa Jam'iyya mai mulki ta APC.

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da mai taikawa shugaban ƙasa Buhari ta ɓangaren yaɗa labarai, Bashir Ahmad, yayi a shafinsa na dandalin sada zumunta wato Facebook.

Bashir Ahmad, ya rubuta a shafinsa cewa: "Zamfara ta dawo gida, lale marhabun gwamna Matawalle."

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta magantu kan yunkurin hana shigo da tukunyar gas Najeriya

A wani labarin, Rikici a jam'iyyar PDP reshen jihar Anambra ya ƙara tsananta yayin da aka bayyana yan takarar gwamna biyu daga ɓangarorin jam'iyyar biyu, bayan gudanar da zaɓen fidda ɗan takara a wurare mabambanta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ugochukwu Uba da Valentine Ozigbo sune yan takarar da aka bayyana daga ɓangarorin jam'iyyar PDP biyu a jihar, kamar yadda thisdaylive ta ruwaito.

Ɗaya daga cikin ɓangaren jam'iyyar bisa jagorancin Chukwudi Umeaba, sun gudanar da zaɓen fidda ɗan takara a makarantar firamare da sakandire dake Awka, inda aka bayyana Uba, ɗan uwan Chris Uba, a matsayin ɗan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel