Siyasar Kano: Jerin Wadanda Ake Kyautata Zaton Za Su Gaji Kujerar Ganduje a 2023
- Zabe na kara karatowa, gwamnoni da sauan 'yan siyasa na bayyana manufofinsu na 2023
- Gwamna Ganduje a jihar Kano, ya bayyana yadda lamarin zaben gwamna zai kasance a can
- A cewarsa, shi ba zai tsayar da wani takarar gwamna ba, wakilai daga jam'iyya su za su yi
Gabanin zaben gwamna a 2023 a jihar Kano, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce wakila da jam'iyya ne za su tsayar da wanda zai fito a matsayin wanda zai gaje shi.
Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan na Kano ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da ‘yan jarida a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni.
Legit.ng ta tattaro cewa Gwamna Ganduje ya yi wannan bayanin ne bayan tsoffin ‘yan takarar gwamna uku a zabukan da suka gabata a karkashin jam’iyyun siyasa daban-daban sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Najeriya Za Ta Buga Wa Kasar Gambia Kudade, Ba Sauran Kai Wa Turai
Wadanda ake sa ran su za su gaji kujerar gwamnatin Kano ta Ganduje a 2023
- Salihu Sagir Takai
- A.A. Zaura
- Umar Yakubu Danhassan
- Nasiru Gawuna, mataimakin gwamnan jihar Kano
- Bara’u Jibrin, sanata mai wakiltar Kano ta Arewa
Gwamnan ya kuma yi ishara da cewa wakilai ne daga jam'iyyar APC za su tsayar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, Daily Independent ta ruwaito.
Gwamna Ganduje ya magantu kan batun yin ritayarsa daga siyasa
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce mai yiwuwa ba zai yi ritaya daga siyasa ba nan kusa, duk da cewa ya shiga siyasa tun 1978, Daily Nigerian ta ruwaito.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a yayin wata tattaunawa da mambobin kungiyar 'yan jarida ta Kano a gidan gwamnati.
Wannan na zuwa ne biyo bayan sanarwar da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, wanda ya bayyana zai fice daga siyasa a shekarar 2023, Nigeria Tribune ta ruwaito.
A nasa martanin, Mista Ganduje ya ce lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan. “A yanzu, ban gaji ba. Ko na yi ritaya ko kada na yi, lokaci zai nuna.
Bari in fada muku cewa na shiga siyasa tun shekarar 1978. "Don haka, ko da na ce zan yi ritaya, idanuna za su ci gaba da kallo, kuma kunnuwana za su ci gaba da ji," in ji shi.
KU KARANTA: Me Ya Rage Nake Nema: Masari Ya Ce Daga 2023 Zai Yi Sallama da Siyasa
A wani labarin, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya hana tara 'yan daban siyasa a wuraren taruka a fadin jihar Kano.
Ganduje, wanda ya sanar da dakatarwar ne ta bakin Babban Sakatarensa na yada labarai, Abba Anwar, a cikin wata sanarwa a karshen mako, Punch ta ruwaito.
Ya ce shawarar ta biyo bayan makamai da suka hada da sanduna, takubba, wukake da adduna da 'yan daba suka rike a yayin wani taron a Kano.
Asali: Legit.ng