'Yan yankin Neja Delta sun ba Buhari wa'adin kwanaki 90 ya sake fasalin Najeriya
- Yankin Neja Delta ya bayyana bukatarsa ga sauya fasalin Najeriya zuwa yadda suke so
- Shugabannin yankin sun bayyana cewa, sun ba da gwamnatin Buhari wa'adin watanni uku don aiwatar da bukatarsu
- A bayan shugaba Buhari ya amince da sauya fasalin kudin tsarin mulkin Najeriya wanda tuni aka fara shiri
Yankin Neja Delta na kudu maso kudu a Najeriya ya aika sako mai karfi zuwa ga gwamnatin tarayyar Najeriya.
Shugabannin yankin bayan wani taron da suka yi a Fatakwal birnin jihar Ribas, a kokarin da suke na mayar da bukatarsu ta gida zuwa sabuwar hanyar yin abubuwa a kasar, sun ba gwamnatin tarayya wa’adin watanni uku don fara aikin sake fasalin Najeriya.
Shugabannin sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da APC ke jagoranta da ta shirya taron tattaunawa na kasa da nufin tsara sabuwar hanya ga kasar, jaridar The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA: Wata Sabuwa: Sojoji sun afkawa ofishin 'yan sanda domin kubutar da masu laifi
A cikin sanarwar da aka fitar bayan taron a Port Harcourt, shugabannin sun ce sake fasalin kasar ya zama dole domin inganta kasar.
Da suke ci gaba da bayani, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da rarraba iko ga jihohi.
Hakanan, shugabannin sun sha alwashin daukar mataki kan nuna karfi da danniya ga yankin Neja Delta da mutanensa.
Wani sashen sanarwar ya ce:
“Mu mutanen Neja Delta muna ba Gwamnatin Najeriya wa’adin watanni uku don magance matsalolinmu game da sake fasalin kasa, ta hanyar kiran taron kasa na wakilan kabilun Najeriya don tsara sabuwar hanya ga kasar.
"Mu mutanen Neja Delta muna bukatar a sake fasali, tare da jihohi a matsayin sassan tarayya da kuma rarraba karin iko ga jihohin."
Gwamnatin tarayya ya kamata ta daina sayarwa China dukiyar Najeriya
Hakazalika, shugabannin sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta daina sayarwa China da dukiyar kasar.
"Mutanen Neja Delta sun bukaci gwamnatin tarayya da ta daina sayar da albarkatunmu ga kasashen China ko Sukuk masu tallatawa, don tabbatar da karbar wani kwangila."
Buhari ya amince da yunkurin sake fasalin kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da kofa ga duk wani kwaskwarima ga Kundin Tsarin Mulki na 1999 kan sake fasalin kasa.
Ya yi wannan bayanin ne lokacin da shugaban kungiyar Ijaw National Congress (INC), karkashin jagorancin Farfesa Benjamin Okaba, ya ziyarce shi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaban ya lura cewa majalisar kasa, wacce nauyin gyara kundin tsarin mulki ke wuyanta, ta kammala shawarwarin tsakanin yankuna.
KU KARANTA: A Cire Tallafin Man Fetur Sai Najeriya Ta Ci Gaba, Minista Ya Fadi Dalilai
Kungiyar ESN Ta Kashe Bokanta Bisa Yin Tsafin da Bai Yi Tasiri Kan ’Yan Sanda Ba
A wani labarin, Mambobin haramtacciyar kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) sun harbe wani mutum, mai suna Paschal Okeke, wanda ke kera “layar cin nasara” ga kungiyar saboda gazawar layarsa wajen karesu na tsawon shekaru, in ji ‘yan sanda a jihar Imo.
Wata sanarwa daga ‘yan sanda ta ce, kungiyar ta fusata da cewa layar, wanda ya kamata ta sa ba za a iya cin nasara a kansu ba kuma su tsere wa farmakin jami’an tsaro ba ta yi wani tasiri ba.
‘Yan sanda sun ce kisan ya biyo bayan samun nasarar 'yan sanda na kai samame a maboyar kungiyar da kuma ragargazar mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng