Shugaba Buhar Ya Gwangwaje Tawagar Yan Ƙwallon Najeriya da Kyautar Sabbin Gidaje

Shugaba Buhar Ya Gwangwaje Tawagar Yan Ƙwallon Najeriya da Kyautar Sabbin Gidaje

  • Buhari ya amince a baiwa tawagar yan ƙwallon Najeriya waɗanda suka ci ƙasar AFCON 1994 a Tunusia kyautar gidaje
  • Buhari ya bayyana haka ne a wani jawabi da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Alhamis
  • Mr. Shehu yace shida daga cikin yan wasan tare da wasu mutum uku sun riga sun amshi nasu tun a baya

Shuagaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya amince a baiwa tawagar yan ƙwallon Najeriya gidaje masu ɗakin kwana uku, waɗanda suka zama zakara a ƙasar kofin africa AFCON a shekarar 19194, a Tunusia, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ma'aikatan SPW: Mun Kammala Biyan Akalla Mutum 400,000 Haƙkinsu Na N60,000, Keyamo

Kakakin shugaban ƙasa, malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Alhamis, wanda aka yiwa take da "Buhari ya bada kyautar gida ga yan kwallon super eagles da suka ci AFCON 1994", kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Tawagar yan wasan Najeriya a 1994
Shugaba Buhar Ya Gwangwaje Tawagar Yan Ƙwallon Najeriya da Kyautar Sabbin Gidaje Hoto: @muhammadubuhari
Asali: Instagram

Wani sashin jawabin yace: "Shugaba Buhari ya amince da kyautar gida mai ɗakunan kwana uku ga kowane daga cikin tawagar yan ƙwallon Najeriya waɗanda suka ci gasar AFCON 1994."

"Buhari ya cika alƙawarin da gwamnatin tarayya ta ɗaukar musu na basu kyautar gidaje."

KARANTA ANAN: Bayan Ganawa Da Buhari, Gwamna Bagudu Ya Bayyana Sunan Waɗanda Suka Sace Ɗaliban FGC Yauri

"Biyo bayan wani kundi da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya gabatar, shugaba Buhari ya amince ya baiwa kowannen su gida a johohin su, amma yan wasa shida da yan tawagar bada horo uku sun riga sun amshi na su tun a baya."

A wani labarin kuma Mun Ɗauki Tsauraran Matakai Ta Yadda Ba Za'a Sake Kai Hari Makarantun Mu Ba, Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa tana iya bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da tsaro a makarantun jihar

Kwamishinan jin ƙai da walwala, Hajiya Hafsat Baba, ita ce ta bayyana haka a wurin wani taron da ma'aikatarta ta shirya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262