Gwarazan Yan Sanda Sun Yi Artabu da Yan Boko Haram, Sun Kuɓutar da Matafiya da Dama

Gwarazan Yan Sanda Sun Yi Artabu da Yan Boko Haram, Sun Kuɓutar da Matafiya da Dama

  • Jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakar yan Boko Haram a kan hanyar Maiduguri zuwa Kano
  • Jami'an RRS tare da taimakon yan sanda sun fafata da yan ta'addan yayin da suka kuɓutar da matafiya da dama
  • Wata majiya mai ƙarfi daga cikin waɗanda lamarin ya shafa sun tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai

Wata tawagar jami'an tsaro bisa jagorancin yan sanda sun yi artabu da yan Boko Haram, inda suka kuɓutar da mutane da dama, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Lamarin ya faru ranar Jumu'a, kuma daga cikin jami'an tsaron har da jami'an ko ta kwana (RRS) na gwamnatin jihar Borno.

KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Hallaka Matar Wani Tsohon Kwamishina

Wasu daga cikin waɗanda aka kuɓutar da kuma jami'an RRS sun tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Jami'an tsaro sun daƙile harin yan Boko Haram
Gwarazan Yan Snda Sun Yi Artabu da Yan Boko Haram, Sun Kuɓutar da Matafiya da Dama Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yan ta'addan sun kai hari ne kan hanyar Maiduguri- Kano da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Jumu'a.

Wannan harin shine na farko da aka kai kan wannan hanyar tun watan Fabrariru, lokacin da wasu yan bindiga suka sace matafiya da dama a hanyar.

RRS ne suka jagoranci fafatawar

Jami'an RRS, bisa jagorancin kwamnadansu, Abioye Babalola, sun yi gaggawar kai ɗauki biyo bayan kiran gaggawa da wasu matafiya da suka tsere daga wurin harin suka yi.

Wata majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa yan bindiga sun kai harin kan hanyar bayan sun fafata da wasu jami'an yaki da ta'addanci na hukumar yan sanda.

Majiyar tace Maharan haye a motocin yaƙi aƙalla biyar sun tare motocin matafiya da dama yayin da wasu suka fita daga motocinsu suka tsere cikin daji.

KARANTA ANAN: Bayan Ganawa Da Buhari, Gwamna Bagudu Ya Bayyana Sunan Waɗanda Suka Sace Ɗaliban FGC Yauri

A cewar majiyar: "Yayin da yan bindigan suka tare matafiya, waɗanda suka kasa guduwa, ba zato ba tsammani sai jami'an RRS suka kawo ɗauki, inda suka yi musayar wuta da yan ta'addan."

"Hakan ya tilasta wa yan ta'adan tserewa suka bar fasinjojin da suka yi niyyar sace wa."

Da yake jawabi a wayar tarho, kwamandan RRS, Mr Babalola, yace:

"Mun yi aikin da aka ɗora mana ne kawai, lamarin ya faru a Garin Kuturu, kilomitoci ƙaɗan kafin ka isa Auno. Mun kai dauki wajen ne bayan samun rahoto daga wasu mazauna yankin."

"Amma da muka isa wuirin, mun fahimci sun yi artabu da wasu jami'an yan sanda, kuma sun zagaye wasu fasinjoji, saboda haka muna isa muka buɗe musu wuta sannan muka yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye."

"Hakan ya tilastawa maharan tserewa suka bar fasinjojin da suka yi niyyar sace wa anan."

A wani labarin kuma Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya ƙara jaddada maganarsa kan cewa duk wanda ya ɗauki makami ya yaƙi Najeriya zai fuskanci hukunci

Shugaban yace matasa na da rawar da zasu taka domin gina goben su da kuma ƙasar su, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: