'Yan bindiga sun yi awon gaba da mataimakin shugaban ƙaramar hukuma a Kaduna

'Yan bindiga sun yi awon gaba da mataimakin shugaban ƙaramar hukuma a Kaduna

  • Yan fashi da makami sun yi garkuwa da Mataimakin Shugaban karamar hukumar Jaba da ke Jihar Kaduna, James Bijimi
  • Har ila yau maharan sun yi awon gaba da wasu karin mutane da ba a san adadinsu ba
  • Kakakin yan sandan jihar, Jalige ya ce jami'an tsaro sun kwace abin hawa guda uku mallakar 'yan fashin tare da raunata mutum ɗaya

‘Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Jaba da ke Jihar Kaduna, Mista James Bijimi da wasu matafiya da ba a tantance yawansu ba a kan hanyar Kaduna zuwa Kachia.

Lamarin ya zo ne kwanaki biyu bayan da ‘yan bindigar suka kashe wani direba suka kuma yi garkuwa da wasu mutane 33 a cikin garin na Kachia.

KU KARANTA KUMA: MKO Abiola ya kasance a ofishina a lokacin yakin neman shugabancinsa na 1993, Garba Shehu

'Yan bindiga sun yi awon gaba da mataimakin shugaban ƙaramar hukuma a Kaduna
'Yan fashin daji sun yi garkuwa da mataimakin shugaban ƙaramar hukuma a Kaduna Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bakin kakakinta, Mohammed Jalige ta tabbatar da faruwar lamarin amma ba ta bayar da adadin wadanda aka sace ba, Channels TV ta ruwaito.

Ya ce jami'an tsaro sun gano motoci uku da alama na wadanda aka sace ne, yayin da mutum daya ya ji rauni.

Sai dai, wani shugaban yankin da ba ya son a ambaci sunansa, ya fada wa gidan talabijin na Channels cewa:

"'Yan fashin sun yi shinge a kusa da Gonan Roger da Makyali a karamar hukumar Kajuru da misalin karfe 10:00 na safiyar Juma'a, inda suka tare wasu motoci sannan kuma suka tafi da wasu mutane ciki har da Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Jaba."

Ya ce jami'an tsaro sun hanzarta kai dauki yankin kuma sun fafata da 'yan bindigar.

A halin yanzu, yayin arangamar, sojojin sun sami nasarar ceto wasu mata shida da aka sace.

KU KARANTA KUMA: Abokai uku sun kera mota mai tafiya a kan ruwa ta hanyar amfani da kayan gida, bidiyon ya birge mutane da yawa

Wani babban jami'in karamar hukumar ya kuma shaida wa gidan talabijin din cewa 'yan fashin sun kulla alaka da dangin Mataimakin Shugaban da aka sace, kuma suna neman kudin fansa na Naira miliyan 100 kafin a sake shi.

A gefe guda, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yaba da kokarin da sojojin Najeriya na Brigade 3 suka yi na tsare dajin Falgore da wasu sanannun gandun daji a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin 1 Division Nigerian Army na Kaduna, Ezindu Idimah ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Kaduna.

Mista Idimah ya bayyana cewa tsare gandun dajin da sojoji suka yi ya hana masu aikata laifuka 'yancin aiwatar da munanan ayyukansu a ciki da kewayen wadannan dazukan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel