MKO Abiola ya kasance a ofishina a lokacin yakin neman shugabancinsa na 1993, Garba Shehu

MKO Abiola ya kasance a ofishina a lokacin yakin neman shugabancinsa na 1993, Garba Shehu

  • Wataƙila yawancin 'yan Nijeriya ba su san cewa Garba Shehu abokin marigayi MKO Abiola wanda ya ci zaɓen 1993 bane
  • Mai taimaka wa Shugaban kasa a kafafen yada labarai ya bayyana wannan dan boyayyar gaskiyar a cikin wani sakon da ya wallafa a Facebook
  • Shehu ya kuma bayyana cewa Abiola ya dauki nauyin karatun wani malamin sa wanda daga baya ya yi ma sa yakin neman zabe

Wani hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya magantu a kan haduwarsa da marigayi MKO Abiola a shekarar 1993 kafin zaben shugaban kasa.

A wani sako da ya wallafa a shafin Facebook a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, Shehu ya ce ofishin sa a matsayin babban manajan kamfanin buge-bue na Janar Triumph shi ne wuri na farko da dan siyasar ya yada zango a lokacin da ya zo Kano don kamfen din sa.

KU KARANTA KUMA: Abokai uku sun kera mota mai tafiya a kan ruwa ta hanyar amfani da kayan gida, bidiyon ya birge mutane da yawa

MKO Abiola ya kasance a ofishina a lokacin yakin neman shugabancinsa na 1993, Garba Shehu
Shehu ya ce dan siyasan na kasar Yarbawan ya saki jiki sosai a ofishinsa Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Hadimin Shugaba Buhari ya lura cewa Abiola ya saki jiki sosai a ofishinsa har ya sauke babbar rigarsa kan kujera ya huta kafin ya ci gaba da gangamin da shirya.

Shehu ya kara da cewa wanda ya lashe zaben na ranar 12 ga watan Yuni ya kuma dauki nauyin karatun digirin digirgir na wani Faruk Umar wanda ya kasance malaminsa na kwaleji.

KU KARANTA KUMA: Muna Godiya: Ganduje Ya Jinjina Wa Sojoji Bisa Kare Dajin Falgore da Jihar Kano

Ya bayyana cewa wannan karimcin daga marigayi Abiola ya sanya Umar shiga kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasar kusan a nan take.

Kalamansa:

"Lokacin da marigayi Cif MKO Abiola ya zo Kano yin kamfe a shekarar 1993, zangonsa na farko ya kasance a ofishina a matsayin Janar Manaja, Kamfanin buge-buge na Triumph.
"Ya fuskanci 'yan jarida a cikin wata hira kuma ya yi magana da ma'aikata da sauran masu sha'awar aikinsa a cikin harabarmu kamar yadda aka nuna a hoton.
"Dakta Faruk Umar, wanda aka gani a hoto tare da ni muna sauraren marigayi zababben Shugaban kasar na Najeriya shi kansa ya ci gajiyar ayyukan alheri na MKO. Ya biya kudin da Faruk ke bukata don kammala karatun digirin digirgir a kasar waje. Don kansa, Faruk wanda shi ne malamina a kwaleji ya ba da kansa a matsayin dan sahun gaba a kamfen din."

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce jam'iyyar APC ta dawo kamar yadda take kuma ta tsallake dukkan matsalolin dake cikin jam'iyyar.

Shugaban kasar ya ce jam'iyyar ta farfado, cike da karfinta kuma ta gyara komai na cikin gida domin zabukanta na gaba, The Cable ta ruwaito.

Buhari ya sanar da hakan a ranar Juma'a a wani taron da yayi da kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC wanda ke samun shugabancin Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng