Abokai uku sun kera mota mai tafiya a kan ruwa ta hanyar amfani da kayan gida, bidiyon ya birge mutane da yawa
- Abokai masu hazaka guda uku sun kera wata kyakkyawar mota wacce za'a iya tukawa a kan ruwa sannan a baje ta
- A cikin wani bidiyo da ya shahara, an hasko hazikan suna gwada motar da suka kirkira akan teku
- Motar su wacce ke da zane kamar kowacce irin mota da ke bin hanyoyi ta ba mutane da dama sha’awa
Abokai uku sun baje kolin motocin da suka kera mai ban mamaki.
Mutanen da ba a san ko su wanene ba, a cewar TRT World sun kirkiri motocin da ke tafiya a kan ruwa da kansu.
KU KARANTA KUMA: Amurka: An yankewa dan sandan da ya kashe bakar fata Floyd shekaru 22.5 a gidan yari
Legit.ng ta tattaro cewa motar anyi ta ne ta hanyar amfani da kayan gida.
Ya zuwa yanzu, sun sami damar kera iri-irinta guda 12 a kasar Misira kuma sun samu masu son irin motocin da yawa.
KU KARANTA KUMA: Dan Achaba ya gudu daga asibiti bayan samun labarin matarsa ta haifi ’yan biyu
Abun ya birge masu amfani da yanar gizo
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun nuna sha’awarsu game da wani bidiyo da ke nuna yadda ake gwajin motocin a kan teku. Da yawa sun yi mafarkin mallakar guda daya.
@ fayyazulhassan_786 ya yi martani:
"Na riga na tuka wannan motar akan wasan GTA saboda haka ba sabon abu bane a gareni."
@thisisparkhay ya ce:
"Lokacin da kuke kiran shi mota, yana nufin shi ma yana iya tafiya a kan hanya? idan ba haka ba ta yaya za ku kira shi abin hawa? Kawai jirgin ruwa ne wanda aka tsara da fasalin mota."
@nurlyanamustapa yayi tsokaci:
"Kuma har yanzu ina jiran mota mai tashi ..."
A wani labarin, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya amshi motar Kona mai aiki da Wutar Lantarki wacce Hukumar Kula da kera motoci da cigaban motoci ta kasa (NADDC) tare da hadin gwiwar kamfanin Stallion suka bude kwanan nan.
Ku tuna cewa a ranar 5 ga watan Fabrairu, NADDC, a karkashin jagorancin Darakta-Janar na ta, Jelani Aliyu, ta gabatar da motar mai aiki da lantarki ta farko da aka kera a cikin gida mai suna Hyundai Kona, a Abuja.
Motar an sanya mata farashin Naira miliyan 24 ga kowane daya, tare da ba da garantin batir da kira na tsawon na shekara 5, 100% aiki da lantarki, ba amfani da mai za kuma a iya cajinta a gida da wajen aiki, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng