Da dumi-dumi: Buhari na ganawar sirri tare da shugaban riko na jam'iyyar APC
- Shugaba Buhari ya gana da shugaban riko na jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe
- Buhari Sallau, mai taimaka wa shugaban na musamman kan kafofin yada labarai ne ya tabbatar da wannan ci gaban a cikin wata sanarwa
- Ana sa ran tattaunawar tsakanin gwamnan da shugaban Najeriyan za ta mayar da hankali ne kan rahoton ci gaban da ya shafi jam'iyyar mai mulki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe kuma shugaban kwamitin kula da tsare-tsaren taron jam'iyyar APC (CECPC).
Buhari Sallau, mai taimaka wa shugaban kasa kan kafafen yada labarai ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a Facebook a ranar Juma’a, 25 ga Yuni.
KU KARANTA KUMA: Hare-haren yan fashi: Fusatattun masu zanga-zanga sun hana shige da fice a birnin Gusau na jihar Zamfara
An tattaro cewa shugaban na Najeriya ya yi ganawar tare da Buni wanda ya samu rakiyar mambobin kwamitin rikon na kasa a fadar gwamnati.
Legit.ng ta tattaro cewa shugaban Najeriyan yayin ganawarsa da kwamitin rikon jam’iyyar APC na kasa ya karbi rahoton ci gaba daga shugabanta.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dage tafiyar da ya shirya yi zuwa Landan
Ana tsakar rikici a Jihohi, APC za ta sa lokacin da za ayi zaben Shugabanni na kasa
A wani labarin, mun ji cewa alamu su na nuna cewa akwai yiwuwar gudanar da babban taron APC na kasa a watan Oktoban bana.
Punch ta bayyana wannan a wani dogon rahoto da ya fito. Wani daga cikin jagororin jam’iyyar APC mai mulki a kasa ya zanta da manema labarai ba tare da ya bari an bayyana sunansa ba, ya ce dole taron ya kai Oktoba.
Ganin yadda ake fuskantar kalubale na rajistar ‘ya ‘yan jam’iyya da wasu matsalolin, wannan jigo na jam’iyyar ya ce kiran gangamin kafin Okotoban ba zai yiwu ba.
Asali: Legit.ng