Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dage tafiyar da ya shirya yi zuwa Landan
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage tafiyar da ya shirya yi zuwa Landan saboda wani boyayyen dalili
- Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya bayyana cewa za a sanar da sabuwar ranar yin tafiyar
- Da farko dai Buhari ya shirya tafiya Landan a yau Juma'a, 25 ga watan Yuni domin ganin likita
Rahotanni da muke samu daga fadar shugaban kasa ya nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage tafiyarsa zuwa Landan don ganin likita har sai baba-ta-gani.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yarda zai amince da dokar sake fasalin kasa idan 'yan majalisun tarayya suka zartar
Ya ce:
"An dage tafiyar duba lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa kasar Burtaniya da aka shirya gudanarwa a yau, Juma'a, 25 ga Yuni, 2021."
"Za a sanar da sabuwar ranar da ta dace."
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC mai mulki, ya gana da Buhari
Rotimi Adebayo ya ce:
"Da fatan Allah ya karawa Shugaban kasa lafiya."
Winner Ifeanyi Orji ya ce:
"Sakon bai cika ba ai. Menene dalilin yin irin wannan jinkirtawar kwatsam? Shin akwai wani taron gaggawa da zai halarta ne ko menene? Da wannan zai sa mu tafa masa sosai."
Ndianabasi Udofia ya yi martani:
"Dukkan godiya ta tabbata ga Allah."
Shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiyarsa
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai sake komawa birnin Landan a kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa Buhari zai tafi ne ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, 2021.
Yace Buhari ba zai dawo ba sai bayan makonni biyu.
Asali: Legit.ng