Hare-haren yan fashi: Fusatattun masu zanga-zanga sun hana shige da fice a birnin Gusau na jihar Zamfara
- Hare-haren 'yan bindiga ya tilastawa fusatattun matasa a Bungudu da kewaye da ke Jihar Zamfara fitowa babbar titin Gusau
- Mutanen sun fito ne domin yin zanga-zanga inda suka rufe babbar hanyar shiga birnin Gusau
- Lamarin ya haifar da cunkoson ababen hawa a safiyar yau Juma'a, 25 ga watan Yuni
Rahotanni sun kawo cewa fusatattun matasa a garin Bungudu da kewaye da ke Jihar Zamfara sun rufe babbar hanyar shiga birnin Gusau domin nuna fushinsu kan hare-haren 'yan fashin daji da suka addabe su.
An tattaro cewa mutanen garin wadanda mafi akasarinsu mata ne da yara sun toshe hanyar a safiyar yau Juma’a, 25 ga watan Yuni, sannan suka haddasa cunkoson ababen hawa.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC mai mulki, ya gana da Buhari
Wannan al’amari ya sa babu shige da fice daga Gusau, babbar birnin jihar ta Zamfara.
A hirarsu da sashin BBC, masu zanga-zangar sun bayyana cewa sun fito ne bisa tsoron hare-haren 'yan bindiga bayan sojojin da ke bai wa garinsu tsaro sun yi kaura daga garin.
Sai dai kuma babu tabbaci a kan wannan ikirari nasu.
Sashin labaran ta nakalto wani mutum da aka sakaya sunansa yana fadin cewa 'yan bindigar sun kashe soja ɗaya da ɗan sanda ɗaya a harin da suka kai kasuwar Bingi sannan suka ƙone ta ƙurmus tare da ɗibar kayayyakin mutane.
Ya ce mutanen sun yi tafiyar kusan kilomita 30 tare da kayayyakinsu kafin suka fito bakin babban titin.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC mai mulki, ya gana da Buhari
Sojoji sun tare shanun sata 154, sun damke miyagu 44 a Zamfara
A wani labarin, rundunar Operation Hadarin Daji, ta tare motoci manya 12 dankare da shanu 154 tare da kame miyagu 44 a jihar Zamfara, Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Mataimakin kwamandan rundunar, Air Commander Abubakar Abdulkadir, ya sanar da hakan a Gusau a ranar Juma'a yayin mika shanun satan ga gwamnatin jihar Zamfara.
Abdulkadir ya ce an kama wadanda ake zargin ne yayin da suke tafe da shanu 154, rakumi daya da kuma rago daya a manyan motoci kan hanyarsu ta zuwa Gusau.
Asali: Legit.ng