Ana tsakar rikici a Jihohi, APC za ta sa lokacin da za ayi zaben Shugabanni na kasa

Ana tsakar rikici a Jihohi, APC za ta sa lokacin da za ayi zaben Shugabanni na kasa

  • Bisa dukkan alamu sai an kai akalla watan Oktoba kafin APC ta shirya gangaminta
  • An tsara shugabannin rikon kwarya za su gudanar da zaben shugabanni a watan nan
  • Akwai aiki a gaban Kwamitin Mai Mala Buni kafin su iya shirya zaben shugabanni

Alamu su na nuna cewa akwai yiwuwar gudanar da babban taron APC na kasa a watan Oktoban bana. Punch ta bayyana wannan a wani dogon rahoto da ya fito.

Wani daga cikin jagororin jam’iyyar APC mai mulki a kasa ya zanta da manema labarai ba tare da ya bari an bayyana sunansa ba, ya ce dole taron ya kai Oktoba.

Ba zai yiwu ba - Wani kusa a jam'iyyar APC

Ganin yadda ake fuskantar kalubale na rajistar ‘ya ‘yan jam’iyya da wasu matsalolin, wannan jigo na jam’iyyar ya ce kiran gangamin kafin Okotoban ba zai yiwu ba.

KU KARANTA: Wasu matsaloli 7 da APC ta ke fuskanta a jihar Kano

Shugabannin jam’iyyar suna kuma kokarin sulhunta rigimar da ta ke cin APC a jihohin kasar nan.

Jaridar ta ce har yanzu kwamitin bai karkare aikin rajistar ba ta yadda za a kira babban taro na kasa. Ana so a gama dinke baraka kafin a shirya zaben shugabanni.

Sannan kwamitin zai yi wahalar nemo kudin da za a shirya wannan taro domin shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba za a taba baitul-mali domin zaben ba.

A lokacin da aka kafa kwamitin Mala Buni a bara, an ba su watanni shida su shirya zabe, bayan wa’adinsu ya cika, sai aka kara masu wasu watanni shidan a Yuni.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta doke PDP a Gwaram, ta maida kujerar Majalisa

APC NEC
Wani taron APC NEC da aka yi a 2019 Hoto: APC
Asali: Facebook

Majiyar ta ce: “Shirye-shiryen wani aiki ne, dole a san inda za ta tatso kudi. Saboda shugaban kasa ya ce ba za ayi amfani da dukiyar gwamnati wajen aikin APC ba.”

Har ila yau, majiyar ta ce sai an tsaida magana a kan duk yankunan da za a kai takara kafin a fara saida fam ga masu sha’awar rike kujeru a jam’iyyar APC na kasa.

Dama can ba da gaske ake yi ba - Concerned APC Members

Mai magana da yawun kungiyar Concerned APC Members, Abdullahi Dauda, ya soki kwamitin, ya ce tun farko dama an san ba za su iya shirya zaben a watan nan ba.

A ranar Lahadi mun kawo rahoto cewa bayan wata da watanni ana ta faman rigima a APC ta reshen jhar Kwara, fusatattun ‘Yan Jam’iyya sun fice daga jam'iyyar.

Bayan sulhu da bangaren Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya gagara, wasu kusoshi da 'ya 'yan APC akalla 20, 000 a jihar Kwara sun ce sun yi sallama da Jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel