Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiyarsa gobe

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiyarsa gobe

  • Shugaban kasa zai sake zuwa Landan ganin Likitansa
  • Kamar tafiyar farko, zai kwashe makonni biyu a kasar Birtaniya
  • Har yanzu yan Najeriya basu san takamammen cutar da shugaban kasan ke fama da ita ba

Shugaba Muhammadu Buhari zai sake komawa birnin Landan a kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa Buhari zai tafi ne ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, 2021.

Yace Buhari ba zai dawo ba sai bayan makonni biyu.

KU KARANTA: Dalilin da Buhari da APC suka gaza a cikin shekara hudun farko — Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiyarsa gobe
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiyarsa gobe
Asali: Original

DUBA NAN: Najeriya ta talauce, wajibi ne mu cigaba da karban bashi: Shugaban Majalisa

Adesina yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Landan, kasar Birtaniya ranar Juma'a, 25 ga Yuni, 2021, don sake ganin Likita."
"Zai dawo kasar a mako na biyu a watan Yuli, 2021."

Watan Afrilu Buhari ya dawo daga Landan

Za ku tuna Shugaban na Najeriya, mai shekaru 78, ya dawo kasar ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a daga Landan ranar Alhamis, 15 ga watan Afrilu da rana.

Buhari na fama da wani rashin lafiyan da bai bayyanawa yan Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel