Shugaba Buhari ya yarda zai amince da dokar sake fasalin kasa idan 'yan majalisun tarayya suka zartar
- Kiraye kiraye da ake kan sake fasalin Najeriya sun kara karfi a cikin 'yan watannin da suka gabata a duk fadin kasar
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da alamar cewa ba shi da wata damuwa game da kiraye-kirayen idan har Majalisar Dokoki ta amince da shi
- Shugaba Buhari ya yi watsi da kiranye-kirayen a baya, amma matsayarsa na baya-bayan nan yana nuna cewa ba lallai ne yana adawa da lamarin ba
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 34 ga watan Yuni ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da goyon baya ga duk wani kwaskwarima da aka yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 kan sake fasalin kasa.
Ya yi wannan bayani ne lokacin da shugabannin kungiyar Ijaw National Congress (INC), karkashin jagorancin Farfesa Benjamin Okaba, suka ziyarce shi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC mai mulki, ya gana da Buhari
Ina bibiyar doka har karshe
Shugaban kasar ya bayyana cewa majalisar kasa, wacce nauyin gyara kundin tsarin mulki ya rataya a wuyanta, ta kammala tattaunawa na yanki.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, kuma Legit.ng ta gani ta nakalto Buhari yana cewa:
"Da zaran sun kammala tsarin, ba za a samu jinkiri kan matakin da ya kamata ba a bangarena."
KU KARANTA KUMA: Harin makarantar Kebbi abun damuwa ne, barazana ne ga tsaro a arewa maso yamma – El-rufai
Shugabannin Kudu Ga Buhari: Najeriya Za Ta Mutu Idan Ba a Gyara Fasalinta Ba
A wani labarin, Kungiyar Shugabannin Kudanci da na Tsakiya (SMBLF) a Najeriya ta ce hanya daya tilo da za a bi don kawar da mutuwar Najeriya ita ce a sake fasalin kasar.
Kungiyar a ranar Lahadi ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi wa ’yan Najeriya jawabi kan matsaloli daban-daban da kasar ke fuskanta.
Edwin Clark, shugaban kungiyar SMBLF na kasa, ya bayyana haka a wani taro a Abuja, The Cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng