Shugabannin Kudu Ga Buhari: Najeriya Za Ta Mutu Idan Ba a Gyara Fasalinta Ba

Shugabannin Kudu Ga Buhari: Najeriya Za Ta Mutu Idan Ba a Gyara Fasalinta Ba

- Kungiyar shugabannin kudanci da tsakiyar a Najeriya sun bayyana kokensu ga halin da kasa ke ciki

- Sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya yiwa 'yan Najeriya bayanin yanayin da ake ciki

- Sun kuma bukaci shugaban ya duba yiwuwar sake fasalin Najeriya ba wai yiwa kundi kwaskwarima ba

Kungiyar Shugabannin Kudanci da na Tsakiya (SMBLF) a Najeriya ta ce hanya daya tilo da za a bi don kawar da mutuwar Najeriya ita ce a sake fasalin kasar.

Kungiyar a ranar Lahadi ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi wa ’yan Najeriya jawabi kan matsaloli daban-daban da kasar ke fuskanta.

Edwin Clark, shugaban kungiyar SMBLF na kasa, ya bayyana haka a wani taro a Abuja, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Mun Biya Fansan N180000000 Kafin a Sako 'Ya'yanmu, Iyayen Daliban Greenfield

Shugabannin Kudu Ga Buhari: Najeriya Za Ta Mutu Idan Ba a Gyara Fasalinta Ba
Shugabannin Kudu Ga Buhari: Najeriya Za Ta Mutu Idan Ba a Gyara Fasalinta Ba Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ya ce: “Dalilin wannan taron a fili yake. Ina za mu je a Najeriya? Wasu na neman ballewa, wasu na neman tarwatsewa, wasu na tafiyar da tsarin mulki na bai daya, da sauransu.

“Lokaci yana tafiya cikin sauri kuma akwai bukatar mu bayyana matsayin mu karara ga 'yan Najeriya.

“Shugaban kasa ba sarki bane, ba jagora bane, ba sarkin gargajiya bane, dan siyasa ne. Ya kamata ya fito ya hadu da wasu daga cikinmu wadanda muke nan tun kafin ya kasance soja a can baya.

"Kasar nan tamu ce gaba dayan mu, arewa kadai ko kudu kadai ba za su iya mulkin kasar nan ba.

“Muna son sabon kundin tsarin mulki. Duk wani kwaskwarimar da za a yi wa kundin tsarin mulki, ba ni da kwarin gwiwa akansa.

"Mun zo nan ne don abubuwa biyu: Ya kamata a sake fasalta Najeriya. Shugaba Buhari ya taba cewa idan ba mu kashe rashawa ba, rashawa za ta kashe Najeriya."

“Na ce idan ba mu sake fasalin Najeriya ba za ta mutu. Ballewa ba shine mafita ba. Abu na biyu, muna son tsarin shiyya-shiyya ya ci gaba. Tsarin mulki ne… muna son yankin kudu ya yi mulki a 2023.”

Yankin kudancin Najeriya na ci gaba da fuskantar hare-haren tsageru 'yan bindiga a cikin 'yan kwanakin nan.

A makon da ya gabata, an kone ofisoshin 'yan sanda da na hukumar zabe mai zaman kanta INEC da dama a yankin.

A ranar 18 ga watan Mayu ne wasu 'yan bindiga suka bankawa ofisoshin INEC har biyu wuta a jihar Enugu, The Guardian ta ruwaito.

KU KARANTA: Sharhin 'Yan Najeriya Game Da Mutuwar Tsohon Hadimin Jonathan, Ahmed Gulak

A wani labarin, A yau 30 ga watan Mayu aka harbe fitaccen dan siyasa kuma jigo a jam'iyyar APC, Ahmed Gulak a Owerri, babban birnin jihar Imo, akan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Sam Mbakwe na Kasa da Kasa.

Mutuwar Gulak ta zo ne yayin da ake fama da karuwar rashin tsaro a kudu maso gabas da kudu maso kudu, tare da majiyoyi da suka tabbatar da cewa an kai masa harin ne a cikin motarsa ​​ta Camry mai lamba Texas BFT 2150.

Labarin mutuwarsa ya bayyana ne daga abokin karatunsa, Dakta Umar Ado a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Nigeria Tribune ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.