Ma'aikatan SPW: Mun Kammala Biyan Akalla Mutum 400,000 Haƙkinsu Na N60,000, Keyamo
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kammala biyan aƙalla mutum 400,000 kuɗin su na shirin SPW
- Ƙaramin ministan ƙwadugo, Festus Kiyamo, shine ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai
- Yace shirin ya gunada a ƙananan hukumomi 774 da muke da su a faɗin Najeriya
Ƙaramin ministan ƙwadugo, Mr. Festus Kiyamo, yace sama da yan Najeriya 400,000 sun karɓi kuɗi Naira N60,000 na aikin SPW da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar a shekarar 2021, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Mun Ɗauki Tsauraran Matakai Ta Yadda Ba Za'a Sake Kai Hari Makarantun Mu Ba, Gwamnatin Kaduna
Keyamo ya bayyana haka a wurin taron manema labarai a gidan gwamnati ranar Alhamis, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Keyamo yace shirin wanda aka kirkiro domin sama wa yan Najeriya aikin yi kuma a rage musu raɗaɗin da annobar korona da jefa su.
Yace yazuwa yanzun aƙalla mutum dubu N400,000 sun samu haƙƙinsu na kuɗi naira dubu N60,000.
Mr. Keyamo, yace: "A halin yanzun an rarraba Naira biliyan N24.817 ga yan Najeriya, kuma za'a duba yiwuwar ƙara mutane domin a cimma kudirin mutum 500,000 a rukunin farko."
KARANTA ANAN: Bayan Ganawa Da Buhari, Gwamna Bagudu Ya Bayyana Sunan Waɗanda Suka Sace Ɗaliban FGC Yauri
An gudanar da shirin a faɗin ƙananan hukumomi 774
Ƙaramin ministan ya ƙara jaddada cewa an gudanar da shirin a faɗin ƙananan hukumomin 774 dake Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai cigaba da tabbatar da an gudanar da duk shirye-shiryen da gwamnatinsa ta ƙirƙiro yadda ya kamata.
A wani labarin kuma Wasu Fusatattun Ɗalibai Sun Yi Fata-Fata da Cibiyar Zana Jarabawar JAMB CBT
Hukumar tsaro ta NSCDC ta samu nasarar damƙe wasu ɗalibai huɗu da take zargin sun lalata cibiyar rubuta jarabawa CBT a Otuoke.
Kwamandan jami'an NSCDC ta jihar Bayelsa, Mrs Christiana, ita ce ta bayyana haka ga manema labari.
Asali: Legit.ng