Mun Ɗauki Tsauraran Matakai Ta Yadda Ba Za'a Sake Kai Hari Makarantun Mu Ba, Gwamnatin Kaduna

Mun Ɗauki Tsauraran Matakai Ta Yadda Ba Za'a Sake Kai Hari Makarantun Mu Ba, Gwamnatin Kaduna

  • Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa tana iya bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da tsaro a makarantun jihar
  • Kwamishinan jin ƙai da walwala, Hajiya Hafsat Baba, ita ce ta bayyana haka a wurin wani taron da ma'aikatarta ta shirya
  • Hajiya Hafsat, tace gwamnati ta samar da ingantaccen wuri da yara zasu samu ilimi cikin kwanciyar hankali

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa tana iyakar bakin ƙoƙarin ta wajen samar da tsaro a makarantun jihar domin tabbatar da babu wani abu da ya hana yara samun ilimi duk da ƙalubalen tsaron da ake fama da shi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bayan Ganawa Da Buhari, Gwamna Bagudu Ya Bayyana Sunan Waɗanda Suka Sace Ɗaliban FGC Yauri

Kwamishinan jin ƙai ta jihar, Hajiya Hafsat Baba, ita ce ta bayyana haka a wurin taron da ma'aikatarta ta shirya tare da haɗin guiwar UNICEF.

A cewarta, gwamnati ta ɗauki matakan da ya dace don tabbatar da yara sun samu ingantaccen ilimi a faɗin jihar cikin kwanciyar hankali.

Makarantun jihar Kaduna
Mun Ɗauki Tsauraran Matakai Ta Yadda Ba Za'a Sake Kai Hari Makarantun Mu Ba, Gwamnatin Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tace: "Gwamnatin Kaduna ta yi duk abunda ya dace a ɓangaren ilimi, lafiya da kuma samar da tsaro."

"Gwamnati ta samar da ingantaccen muhallin da yara zasu kuma a tsare su, domin tsare su yana da muhimmanci saboda sune shugabannin gobe."

UNICEF ta yaba wa gwamnatin Kaduna

Shugaban ƙungiyar UNICEF reshen jihar Kaduna, Dr Wilfred Mamah, yace an samu cigaba sosai a ɓangaren kare ƙananan yara a jihar, kuma an samu wannan nasara ne saboda aiki tare da UNICEF ta yi da gwamnatin Kaduna.

KARANTA ANAN: Wasu Fusatattun Ɗalibai Sun Yi Fata-Fata da Cibiyar Zana Jarabawar JAMB CBT

Dr. Mama ya yaba da yadda gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufa'i yake tafiyar da gwamnatinsa.

Yace: "Duk da matsalolin tsaro da suka addabi jihar, mun gamsu kuma mun yi farin ciki da samun ingantacciyar gwamnati dake kula da ƙananan yara."

A wani labarin kuma Dalilin da Yasa Muke Maida Yan Gudun Hijira Gudajensu Duk da Akwai Ƙalubalen Tsaro, Zulum

Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa na maida yan gudun hijira zuwa gidajen su ne saboda su yi noma, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Gwamnan yace an samu nasara sosai a ƙoƙarin da ake na inganta rayuwar yan gudun hijira a jiharsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262